✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amarya ta fasa aure saboda ango ya fadi jarabawar lissafi

Ana cikin biki ta ce ta fasa auren tare da zargin dangin mijin da rufa-rufa kan rashin iliminsa.

Wata amarya ta yi tsallen badake, ta fasa auren a yayin da ake tsaka da bikin daurin aurenta saboda angonta ya fadi jarabawar lissafi.

Amarya Prisha Vihaan da ta shirya wa angon nata mai suna Reyansh Abay jarabawar lissafin ne a yayin bikin aurensu, amma ya gaza cin jarabawar.

“Dangin angon sun boye mana hakikanin matakin karatunsa, amma  kasancewar ’yar uwar tawa mai basira ce, ta gano yadda ake shirin sanya mata lauje cikin nadi”, cewar daya daga dangin amarya Prisha Vihaan.

Tun farko dai Prisha na zargi mijin da za ta aura din da rashin kokari, shi ya sa ta shirya masa jarabawar lissafi, a matsayin hanyar da za ta gwada zurfin iliminsa.

Danginta na zargi dangin mijin tsohon angon da boye musu cewar ba shi da ilimi, shi ya sa suka amince da jarabawar da ’yar tasu ta shirya wa mijin da zata aura din a ranar 1 ga watan Mayu, 2021.

Fasa auren da Prisha ta yi ya ta da kura, inda dangogin biyu suka shiga musayar yawu a tsakaninsu, inda kowanne bangare ke zargin an cuci dan uwansa.

Wannan ba shi ne karon farko da aka fasa auren masoya ba saboda gaza cin jarabawa.

A shekarar 2015 a kasar ta Indiya, wata amarya mai suna Amrita Rao Sunil ta fasa auren angonta mai suna Mahesh Babu saboda gaza cin jarabawar lissafa da ya yi.