✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al’ummar Yahudawa sun shirya wa Musulmi buda-baki a Abuja

al'ummar Yahudawa mazauna Najeriya sun shirya wa Musulmi buda-baki na musamman a Abuja.

A yayin da shirye-shiryen Karamar Sallah suke kankama, al’ummar Yahudawa mazauna Najeriya sun shirya wa Musulmi buda-baki na musamman a Abuja.

Babban Limamin Yahudawa mazauna Najeriya, Rabbi Israel Uzan, ya ce sun shirya wa Musulmi buda-bakin ne sannan suka gayyato Kiristoci domin yaba wa yadda ’yan Najeriya mabiya addinai daban-daban suke zaune da juna lafiya.

Amurka ta kashe jagoran ISIS a Gabas ta Tsakiya

Yau INEC za ta yi taron gaggawa kan Zaben Adamawa

Da yake bayani a wurin taron a ranar Litinin, Rabbi Israel Uzan, ya ce ya yadda ‘yan Najeriya Musulmi da Kiristoci da Yahudawa suke zaune da juna abin yabawa ne.

“Ba za a iya cewa Najeriya kasar Musulmai ce ko ta Kiristoci ba ce ko ta Yahuwa, duk suna zaune da juna.

“‘Yan Najeriya sun da ban sha’awa a yadda suke mu’amala da juna, a harkokin kasuwanci da siyasa da iyali da sauransu, kuma abin da muke gani ke nan a wannan liyafar,” in ji Rabbi Uzan.

A cewarsa, shi kansa zamansa a Najeriya ya bude masa ido inda ya gano cewa wasu abubuwan da jaridu ke yadawa game da bambancin addini a kasar ba haka ba ne.

Da yake bayani a wurin taron buda-bakin, daya daga cikin manyan limaman Abuja, Dokta Muhammad Kabir Adam, ya jaddada muhimmancin assasa zaman lafiya da rungumar juna ta yadda ba za a cutar da wani saboda addininsa ba. Wannan a bayyane yake a Musulunci.

Babban Limamin Masallacin Al-Habibiyah Mosque, Sheik Fuad Adeyemi, ya ce taron ya nuna cewa kowa zai iya gudanar da addininsa ba tare tashin hankali ba.

A nasa bangaren, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen Abuja, Rabaran Timothy Amakon, ya ce bai kamata addini ya zama abin amfani wajen nuna kiyayya ba ga sauran mutane ba.