Mutanen garuruwan Ngalda da Gujuba a Karamar Hukumar Fika a Jihar Yobe, sun koka kan kyan rashin hanyar da ta hade garuruwan biyu.
Rashin kyan hanyar ya sa jama’ar na shan bakar wahala musamman masu tuka motoci da sai an daura wa mota igiya mutane sun ja ta kafin ta iya wuce wa masu tafiya, yayin da masu tafiya a kafa kuma sai sun bi ta kan gadar katako.
Malam Abdullahi Haruna Dumgulwa, Shugaban Kungiyar Muryar Talaka ta Jihar Yobe ya shaida wa Aminiya, yadda suke fama da hanyar da ba ta wuce kilomita 100 ba.
Abdullahi Haruna, ya ce suna shiga sako da lungu don ganin matsalolin al’umma, kuma su gaya wa gwamnati don ta share musu hawaye.
Ya ce gaskiya al’ummar Ngalda da Gujuba suna shan wahala domin idan mota ta taso daga Ngalda zuwa Gujuba ko tana dauke da kaya ko ba ta dauke da kaya sai an daura mata igiya mutane sun ja ta kafin ta wuce wani wurin.
“Hanyar na bukatar taimakon gaggawa don ceto mutanen yankin musammam a wannan lokaci na damina,” inji shi.
Ya ce a lokacin tsohuwar gwamnatin Sanata Bukar Abba Ibrahim, an yi hanyar amma da yake ba ingantacciya aka yi ba ba a je ko’ina ba ta lalace.
Ya ce daga lokacin da aka rantsar da gwamnatin Mai Mala Buni, Gwamnan ya ziyarci wajen ya ganewa idonsa halin da ake ciki ya kuma yi alkawarin zai duba yiwuwar yin hanyar.
A cewarsa tsakanin Ngalda da Gujuba, bai wuce kilomita 100 ba sai kauyuka kamar 25 da suke tsakaninsu kuma hatta gwamnati na samun kudaden shiga daga al’ummar domin manoma ne da makiyaya a yankin.
Ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomin yankin su taimaka, tunda za su fara cin gashin kansu nan ba da dadewa ba.
Sai ya ce gadar katako ce jama’a masu kafa suke bi idan ta karye mutane sukan bi cikin ruwan yana kai wa mutum har kirji.
Ita ma gadar katakon, kungiyar ci gaban garin Dumgulwa ne da sauran jama’a suke karo-karo don gyara ta a yanzu haka kuma tana daf da karyewa.
Daga nan sai ya ce idan mutum ya ga yadda mutanen yankin ke wahala sai ya zubar da hawaye don tausayi, kamar ba lokacin siyasa ake ba.