Edita ka ba ni dama in bayyana takaicina ganin halin kaka-ni-ka yi da kasata ta shiga. Allah Sarki kasata Najeriya. Na bijiro da wannan ne, ganin yadda a kullum sai koma baya kasar take a maimako cigaba. Komabayan kasar nan, bai rasa nasaba da rashin jagoranci nagari a kasa. Shi yasa kullum talaka kuka yake yi, sakamakon rashin ingancin rayuwa, ga shi ba tsaro, ba isashshiyar wutar lantarki, uwa uba rashin ayyukan yi da suka yi katutu ga matasa. Ina mai addu’ar Allah ya ba mu shugabanni nagari da za su iya ciyar da kasar nan a gaba, tare da inganta rayuwar talaka. Daga Aminu dankaduna Amanawa. 09903552221.
Allah Sarki kasata Najeriya!
Edita ka ba ni dama in bayyana takaicina ganin halin kaka-ni-ka yi da kasata ta shiga. Allah Sarki kasata Najeriya. Na bijiro da wannan ne,…