Alhinin aikin hauni
Karka ce wa iyaye da kakanni
Tsororuwar tsauni
Tsakiyar taka tsani
Tsamin tsamiya yai tsanani
Karime-karimen karambani
Karmamin karan danni
Kai-kawon ce-ce-ku-cen karni
Zaurancen zamani
Motsa muka-mukin cin makani
Langabewar lagwani
Laujen nadin lamuni
Lambar lahani
Laftun lambun furanni
Launi-launi
Giringidimin giwaye
Gigiwar gwanaye
Gararambar gaye-gaye
Hayaniyar zubar da hawaye
Iyaye sun iya yaye
Kai waye
kakkarfa yai kaye
Fundun-fundun kamun kifaye
Filfilon fila-filan fuffuken tsuntsaye
Falakin falle filaye
barambaramar beraye
Burgar buzaye
Birinkidimar banzaye
Balbelar belaye
Burgun burtaye
Zugar zabarin zomaye
’Ya’ya da iyaye
Yaren dan goye
’Yan tagwaye-tagwaye
Amare da angwaye
Haurobiyawa
Man kaza ya yi yawa
dan lele ya yi kawa
Adon gari masu juyin takun rawa
Tarairayar kawa-da-kawa
Hajijiyar katantanwa
’Yan dugwi-dugwi na kada ranwa
Suna sauraren sauke sanwa
In sun yi nat ba sa jin tabahuwa
Sai su barke da sowa
Kada dai ai kokowa
Ko a karke da dira wawa
Ai ta tseren laulawa
Hankalin hautsinewa
Hatttara duka ’yan uwa
Surutun sadarwar sandarewa
Subul da bakan sullutu ba kakkautawa
Sabulun salon sollewa
Sukar sakarcin sukurkucewa
Sunce sasarin ingarman sukuwa
Rike bututun amsa kuwwa
Hantari masu kyakkewa
Hannaye su daina karkarwa
Hargitsin hardewar harawa
Rarrashi mahukunta ai ragowa
Lallai mu daina alaye
kiren-karya da lauye-lauye
Shafen bango a lailaye
Shu’umcin shaye-shaye
Shi ke haifar da jaye-jaye
Tsirin tsitaka
Tsiyatakun tsakiyar ka
Kata-katar rani da kaka
Cankar caka
Jikkatar jika da kaka
Na ga kutungwila
Kisan gilla
Da ta haifar da illa
An zo ana wala-wala
Al’umma ta saki bakin lalala
Haurobiyawa na fama da ALHININ AIKIN HAUNI a ’yan makonnin nan, domin kisan gillar masu gidaje ta karade Kudanci da Arewacin kasar nan. Abin takaicin ma shi ne har wata kwararrriyar mai lauye-lauyen dokoki ta caka wa mijinta tsitaka har ya ce ga garinku nan, tamkar dai yadda ta auku tsakanin Mairamu da danBello. Irin wannnan aika-aika ta zama rruwan dare game duniya, tun da a dai makon da ya arce an ruwaito yadda wata uwargidan ta yi yunkurin yi wa maigidanta kisan gilla a Jihar Zaman-fara, amma kafin ya kai gargara aka dauke shi zuwa farfajiyar Bokan Turai.
Ni dai ina ganin akwai bukatar mu bibiyi TSARIN TARAITARAYA da BIYAYYA, ta yadda za mu fasko ko mun baude daga tafarkin iyaye da kakanni, muna ta wuni-wuni, har muka karke da alhinin aikin hauni.
Wannan mai lauye-lauyen dokoki da tta yi wa mijinta kisan gilla, hakika babbar kutungwila ce, domin ta fi sauran wadanda suka tafka ta’asa a kwanon tasarsu sanin ake garkame mai laifi, amma ta yi kememe ta aikata son zuciyarta. HAYANIYA HAYYA-HAYYA KAYA-KAYYA dai ta haifar da zubar da HAWAYE kada dai a maishemu WAWAYE, har an zo ana ta batun WAYE-WAYE, maimakon a yi aiki kai waye, ta yarda a za a kauce wa jaye-jaye.’Yan makaranta masu koyonwatsattsake da falle shafukan mujallu da makalu a makarantar Dodorido da ke cikin Amintaciyar jaridar kasar Haurobiya ni ina ganin ya kamata ja-gaban turken turakun ma’aukarata ya fara bibiyar kundin magabata don daidaita shi da salon tafiyar zamani. Yin hakan ya zama dole, tunda babu ko tantama mun baude daga kan tturba, shi ya sa ake ta make-make an rasa makama.
Lallai mu hada karfi da karfen karafa, mu daina karfa-karfa wajen turke ma’aurata. Sannan akwai bukatar masu ruwa da tsaki wajen gina al’umma su zamto nagargaru madubin dubarudun dubawar masu fuka-fukin tashi, ta yarda za a kauce wa cusa wa juna haushi, har a kai ga naushi da gaba babu fashi.
Kowa ya sani ba kullum ake kwana gado ba, tamkar tsuntsu gado, saboda akwai samu da rashi, a wani jikon ma har sai an ci bashi, an dan ji dama-dama, a daina dama-dama. Matukar dai muna son sallama da salama sai mu yi kokarin nuni da babbar alama, domin samun makama. Kowa ya yi azama.
Irin aika-aikar da ta bijiro wa ma’aurata a kasar nan ya kamata mu daina fashi da mukami don jin dadin farmakar masu fashi da makami, wadanda ke haifar mana da salallami. Mahukunta an rika RAGOWA amma ban da ROWA, ko takun dn mazari a wajen juyin RAWA, ta yadda manya a cikin al’ummma za su zamto masu TSAWATARWA, su kuwa masu fuka-fukin tashi su zamto masu biyayya ga Uba da UWA, domin gudun kutsa kai cikin kungurmin DAWA, mu yi ta takun YANYAWA rani da damina lokacin da ake TSAWA, har mu karke da TSUWWA.wannan ne dalilin da ya sanya nike ta yi muku YEKUWA ko mun daina kwance goddiyar sakarci ta yi ta SUKUWWA!