✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alfijirin kakar wasa mai zuwa ya fara bayyana

Kafar labarai ta BBC ta  ce shuwagabannin kulob din Arsenal sun ce za a sha wahala kafin a iya shawon kan manyan ’yan wasan kungiyar,…

Kafar labarai ta BBC ta  ce shuwagabannin kulob din Arsenal sun ce za a sha wahala kafin a iya shawon kan manyan ’yan wasan kungiyar, matukar Unai Emery ya ci gaba da jan ragamarta.

A can Manchester City kuwa Raheem Sterling ne ke jiran ya ga idan mai horar da ’yan wasa Pep Guardiola zai ci gaba da zama da kungiyar kafin ya iya saka hannu kan sabuwar yarjejeniya.

A wata mai kama da haka, Guardiola ya ce kungiyoyin da ke tunanin kulla yarjejeniya da mai taimaka masa Mikel Arteta irin su Arsenal da Eberton, sun kwana da shirin cewa ba zai bar kungiyar ba akalla sai zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Jose Mourinho na Tottenham na duba yiwuwar sayen mai tsaron bayan Benfica Ruben Dias mai shekara 22, da kuma dan wasan tsakiyar na Sporting Lisbon Bruno Feranades mai shekara 25.

West Ham kuma na tunanin kawo mai horar da ’yan wasan Shefield United Chris Wilder, idan har sun yanke shawarar sallamar Manuel Pellegrini.

Rahotanni sun ce an gargadi Pellegrini kan cewa dole ne abubuwa su sauya, a wata tattaunawa da shugabannin kungiyar.

Ejan din mai tsaron bayan Manchester United Chris Smalling, ya isa Italiya don fara tattaunawa da kulob din AS Roma kan yiwuwar kulla yarjejeniyar ta dindindin da kungiyar, bayan kammala zaman aro da yake yi.