Alaramman almajiran Arewatawa
Mai gamba da gafakar girmamawa
Tsangayar tsarin tsilla-tsilar tsayuwa
Rumurmutsar romon ragon Romawa
Tabahuwa ta hana almajirai karatun biyawa
Da dankoko suke kewayawa
Suna neman abin cika kururu
Na-mujiyarsu yai kuru-kuru
Wai sun karanta babbaku da farfaru
kolo da titibiri na kaiwa da komowa
Inna uwata
Allazi Wahidin
Ni ne dan malam
Ki ba ni abin tauna
Uwardaki na samu gata
Ranar Juma’a
Nakan tuna A’ishatu fil jami’a
Mai kunna sham’a
Ta daga samma’a
kolo na walagigin turmutsitsin jama’a
Bobo da kwambo
Sai dan boko
kolo na laluben na-koko
Lalitar Alaramma ba ko kwabo
Zamani ya shude
Wasunmu sun rude
Sun sanya almajirai sun baude
Su dai a ba su su dan tande
Hangen nesa ya turbude
Mai martaba da rawunna
Ka ga malumma da alluna
kolo ya karke da ganguna
Titibiri na ta laluben abin tauna
Ilimi an yanke masa kauna
Alifun ana Musulimun
Badatun agwagwa ke nan
Arnabun zomo na nan
Fa’un fa’un fatahat baban
Wato bude kofa ke nan
Alaramma mai imani
Ka dauki salon a zamani
Don dora almajirai a tafarkin sani
A inganta aikin iyaye da kakanni
Gardi da kolo su zam masana fanoni
Arewatawa a nai muku gani-gani
Ba kwa tafiya a turbar karni
Ku dai ku samu na cin makani
Ko kuna tuna umarni
Ballantana munana ai musu hani
Alaramman almajiran Arewatawa, a irin wannan zamani matukar kana son daukaka kalmar Allah, kowa ya kara azama wajen bin umarni da hanin Mai-duka, Mai-kowa, Mai-komai, wajibi ne ka surka da tafiyar zamani, wadda ba ta baude daga kan turba ba. Saboda na fasko cewa gidan kowane Shehun shehinnai, matukar ya amsa suna ‘Shehu,’ ba “SHAHO’ ba, tabbas akwai gwanin BOBO DA kWAMBON BOKOKO a gidansa. Kuma akasari a jerin wadanda suka fasko jirgin tafiyar zamani ake samun ‘SHEHU MAGAJIN SHEHU,’ wanda hadafin manufarsa ba ta ta’allaka wajen tara taro da AHU, illa dai kawai al’umma ta yi SAHU-SAHU, don kada a maishe ta HUHUN MA’AHU.
Wata mahanga da na leko ita ce, ALARAMMAN ALMAJIRAN AREWATAWA zai iya tarbiyyantar da ALMAJIRAI su zama ATTAJIRAI, ko MALUMMAN MALAMMAI masu manufa TAKAMAIMAI. Tunda a wannan zamani masu aikata miyagun ta’adu, musamman samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya, sun kware a kutse da dandatsa a shafukan sadarwar na’ura mai kwakwalwa, kun ga ke nan ba a bukatar BADUHU layar zana. Sannan dan dambe da asakala in ya samu cikakken horon zilliya da iya kai naushi ba ya bukatar SAGAU da SHASHATAU. daukacin wadannan al’amura na nuni da cewa kULLE-kULLEN kULUMBOTO DA TSATSUBA DA TSUBBACE-TSUBBACE ba namu ba ne, ballantana har a kai ga TSATSUBAR TSUMBURBURAR TSATSUNBURUN, da ka iya haifar wa mutum mai imani wasan ’YAR BURUM-BURUM da imani, musamman kan al’amuran da suka shafi hani da umarnin Mai-duka.
Batu na ingarman karfen karafan titi taragon layi kwangiri, shirin raba kayan dundume kururu don WARWAREWAR ’YA’YAN HANJI da cikowar TUMBI, sai an yi wa kolo da Titibiri da Gardi babban tanadi. Sannan bayan Alaramma ya horar da su karatun Littafin Allah, wajibi ne a hada musu da ARJAMI, ko in ce a nusar da su tsarin Ajami da Larabci, kamar yadda manyan shehunanmu irin su Na’ibi Sulaimanu Wali da Shaykh dahiru Maiga suka wallafa wagagen littatafai a wannan fanni.
Idan ma ba za a bai wa Alaramma lada da la’adar karatun babbaku da farfaru ba, to wajibi ne a samar masa garka da gayauna ya rika farda, rani da damina. Don ta haka ne kolo da Titibiri da ke hankoron kaiwa ga matsayinsa za su samu tudun dafawa na daga sana’ar abin dogaron gudanar da rayuwa.
’Yan makaranta masu koyon watsattsake da wangale shafukan mujallu da makalu a kasar Haurobiya kun san yadda ake dura wa Arewatawa ashariya ta uwa, ta uba wai sun ki kula da kolo da Titibiri har ma da gargadin garada. Wai kawai mun yasar da su suna ta walagigin da gararamba da dAN kOkON DABGEN dAN kANZO ko dUMAMEN dAN DAGO-DAGON dUNdUME-kURURU, yayin da na-mujiyarsu ya yi kURU-kURU, musamman a lokacin HUNTURU, a wani lokacin kuwa su yi ZURU-ZURU, domin ba su san yadda za su kulla ’yan DABARBARU ba.
A matsayina na babban Direban Alli a wannan farfajiya ta Dodorido da ke cikin Amintaciyar jaidar kasar Haurobiya, ina kira da kARAJIN MURYA ga iyayenmu masu martaba da rawuna da malumma masu alluna da su lalubo hanyar kyautata rayuwar kolo da Titiri, tun kafin su zama gargadin garada mai yawan gardama da rashin sanin makama. Ita Gwamnatin Baban-burin-huriyya akwai bukatar ta samar wa wadannan rukunin al’umma gine-gine na zamani, ta yadda za su samu natsuwa, ko sun daina tsuwwa, ballantana ta TABAHUWA ta daka musuTSAWA!