Alƙalin Alƙalan Nijeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, ya yi ritaya a wannan Alhamis ɗin, 22 ga watan Agustan 2024.
Mai Shari’a Kayode wanda shi ne Alƙalin Alƙalan Nijeriya na 22 zai bar aiki ne bayan cikarsa shekaru 70 a doron ƙasa.
An dai haifi Ariwoola a ranar 22 ga watan Agustan shekarar 1954, inda a yanzu ritayarsa ta zo bayan shafe tsawon lokaci yana aiki a ɓangaren shari’ar ƙasar.
Ya riƙe muƙamai daban-daban a ɓangaren shari’ar Nijeriya, inda ya kai ƙolokuwa a ranar 27 ga watan Yunin 2022.
Ariwoola ya riƙe muƙamin Alƙalin Kotun Ɗaukaka Ƙara tsakanin 2005 zuwa 2011 bayan ɗaga darajarsa daga Alƙalin Babbar Kotun Jihar Oyo.
A ranar 22 ga watan Nuwamban shekarar 2011 ce ya zama Alƙalin Ƙotun Ƙolin ƙasar.
Tsohon Shugaban Nijeriya ne Muhammadu Buhari ya naɗa Ariwoola a matsayin Alƙalin Alƙalan Nijeriya bayan murabus ɗin Mai Shari’a Tanko Muhammad.
Aminiya ta ruwaito cewa a wannan Alhamis ɗin ne kuma aka gudanar da zama na musamman a Kotun Ƙolin da ke Abuja domin girmama shi.
Da yake jawabi a yayin zaman, Ariwoola ya yi kira da a samar da matakan da za a rage wa Kotun Ƙolin nauyi.
Ya bayyana cewa akwai ƙararraki da dama da ke gaban Kotun Ƙoli da ya kamata a dakatar da su a Kotun Ɗaukaka Ƙara.