An bayyana Najeriya a matsayin daya daga jerin kasashen da suka fi yawan mata masu cutar yoyin fitsari a duniya.
Alkaluma na nuna cewa akwai kimanin kaso 7.5 cikin 100 na masu cutar a Najeriya, kwatankwacin mata 332,000 da ke jiran a yi musu aiki baya ga karuwar masu cutar da ake samu da kimanin mata 13,000 a duk shekara.
- Gwamnan Gombe ya zama sabon shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa
- Jama’a sun kashe ‘barawon babur’, sun kone gawarsa a Gombe
Wannan bayani ya fito ne dgaa bakin Shugaban Gidauniyar Fistula Foundation Nigeria, Malam Musa Isa yayin da yake jawabi a wajen bikin ranar yaki da cutar yoyon fitsari ta duniya a Kano, wacce aka saba yi a duk ranar 23 ga watan Mayu.
Malam Musa ya ce a duk shekara, mata masu yoyon fitsari dubu uku kawai ake iya yi wa aiki, lamarin da ya sa aka bar wawakeken gibi na matan da ke cikin damuwar rashin samun waraka a kan lokaci.
“A yanayin da ake ciki yanzu, za a iya daukar tsawon shekaru 100 ba tare da cike wanan gibi ba, don haka wadanan mata za su ci gaba da fuskantar kyama daga al’umma a wasu lukutan ma har daga wajen iyalansu,” in ji shi.
Malam Musa ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta yi duk mai yiwuwa domin taimaka wa rayuwar matan da ke fama da larurar ta yoyon fitsari duba da yawan matan da ke zuwa asibiti don neman magani a kullum.
“Ina kira ga Gwamantin Jihar Knao da ta ba sha’anin kula da lafiyar masu yoyon fitsari muhimmanci ta hanyar yi musu aiki kyauta, ta kuma horar da likitoci da ma’aikatan jinya ’yan asalin jihar a kan wannan cuta.
“Akwai bukatar gwamnati ta daga darajar wannan cibiya ta Laure da ke cikin Asibitin Murtala, kasancewar a yanzu gado 10 ne kadai a cibiyar, lamarin da ke janyo cunkoso wajen yi wa matan aiki.
“Zai yi kyau idan aka kara dakunan kwantar da marasa lafiya tare da zuba isassun gadaje. Haka kuma, akwai bukatar gwamnati ta samar da isassun kayan aiki tare da samar wa da matan nan abin sana’a da za su dogara da kansu kafin da bayan sun warke duba da irin tsangwamar da suke fuskanta a cikin al’umma,” in ji shi.
Yayin da yake karin haske game da dalilan samun cutar, wani likita da ya kwashe shakaru 27 yana gudanar da yi wa mata masu yoyon fitsari aiki a asibitin na Murtala, Dokta Amiru Yola, ya ce ana samun cutar ce ta hanyar doguwar nakuda da kuma rashin samun cikakkiyar kulawa a kan lokaci daga ma’aikatan lafiya da kuma al’adar da mutane ke da ita tana haihuwa a gida a maimakon zuwa asibiti.
Ita ma a nata jawabin, Kwamishiniyar Al’amuran Mata ta Jihar, Dokta Zahra’u Muhammad Umar, ta ce gwamnatinsu ta yi abubuwa masu yawa don ganin ta inganta rayuwar matan da ke fama da cutar.
Masu fama da wannan cuta sun shaida wa Aminiya cewa suna fuskantar matsalar rashin kudin da za su kula da lafiyarsu inda suka yi kira da gwmanati da masu hannu da shuni da su kawo musu dauki.