Iyalan tsohon Gwamnan jihar Oyo Sanata Abiola Ajimbo sun tabbatar da cewa yana nan da ransa.
Hakan na zuwa ne sakamakon fargabar da jita-jitar rasuwar jigon a jam’iyyar APC ta haifar da kuma kiraye-kiraye domin tabbatar da gaskiyar halin da yake ciki.
Surukarsa kuma ‘yar gidan gwamnan jihar Kano Fatima Ganduje ta tabbatar a wani sako da ta wallafa cewa mahaifi na mijinta na nan da ransa.
“Mun gode da sakonninku, amma babanmu na nan da ransa, alhamdulillha. Idan lokaci ya yi tabbas kowa zai mutu, amma dai da sauran lokaci…,” ta wallafa a shafinta ta Twitter a daren Alhamis.
- Jam’iyyar APC ta nada Ajimobi ya zama shugabanta
- Kotu ta tsawaita wa’adin Giadom a matsayin shugaban APC
- Rudani: ‘Sabon shugaban’ APC ya soke tsarin jam’iyya kan zaben Edo
Kazalika mai magana da yawun Ajimobi, Bola Tunji ya karyata labarin rasuwan ubangidan nasa ta shafinsa na Facebook.
“Ku yi watsi da jita-jitar. Rade-radi ne. Muna dai kara yin addu’a,” inji shi.
Yanzu kimanin makonnin biyu ke nan da aka killace Ajimobi sakamakon kamuwarsa da cutar coronavirus.
Shi ne wanda Kwamitin Amintattun jam’iyyar APC ta ayyana a matsayin shugaban jam’iyyar na riko bayan dakatar da Shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole a ranar Laraba.