✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ajantina na tsoron haduwa da Super Eagles – bictor Moses

Shahararren dan kwallon Super Eagles bictor Moses ya ce yana da yakinin kasar Ajantina tana fargabar sake haduwarta da Najeriya a gasar cin kofin duniya.…

Shahararren dan kwallon Super Eagles bictor Moses ya ce yana da yakinin kasar Ajantina tana fargabar sake haduwarta da Najeriya a gasar cin kofin duniya.

Super Eagles dai an sanya ta ne a rukunin D a Gasar Cin Kofin duniya, rukunin da ya kunshi kasashen Ajantina da Kurosiya da kuma Iceland.

kasashe biyu ne da suka fi samun maki a kowane rukuni za su hayewa matakin zagaye na biyu na gasar.

bictor Moses ya ce, ganin yadda Najeriya ta lallasa Ajantina da ci 4-2 yana da tabbacin Super Eagles za ta fito a rukunin D idan aka fara gasar cin kofin duniya.

“Duk da yake mun sha haduwa da kasar Ajantina, amma abin mamakin ne ganin yadda aka sake hada kasar da Najeriya a wannan lokaci.  Muna tsoron haduwa da ’yan kwallo irin su Lionel Messi a zagayen farko na gasar amma duk da haka ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen ganin mun hayea zuwa zagaye na biyu na gasar”.

bictor Moses da Lionel Messi ba su buga wasan sada zumunci a tsakanin kasashen biyu a kwanakin baya a Rasha ba, amma ana ganin za a yi gumuruzu idan kasashen biyu suka hadu a gasar cin kofin duniya.

Tuni masana harkar kwallo suka rika bayyana ra’ayoyinsu game da sake haduwar kasashen biyu.   Yayin da wasu ke ganin Ajantina ce za ta lallasa Najeriya a wasan wasu kuwa gani suke Najeriya ce za ta sake rike wuyan Ajantina a wasan, ganin yadda suka lallasa kasar a wasan sada zumunta ba tare da wata wahala ba.