✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aikin jarida ya zama gado a gidanmu – Yusuf Ladan

Alhaji Yusuf Ladan dan Iyan Zazzau kuma Hakimin Kabalan Doki da ke Kaduna fitaccen dan jarida ne da ya bayyana wa Aminiya cewa aikin jarida…

Alhaji Yusuf Ladan dan Iyan Zazzau kuma Hakimin Kabalan Doki da ke Kaduna fitaccen dan jarida ne da ya bayyana wa Aminiya cewa aikin jarida ya zama gado a gidansu, domin mahaifinsa  marigayi Alhaji Muhammadu Ladan (MON) ne kwanturola na rediyo na farko a Arewa. Sannan dansa Abubakar Ladan yanzu haka yana aiki a gidan Rediyon Tarayya na Kaduna. Wakilinmu ya tattauan da shi kan rayuwarsa da gwagwarmayarsa a fagen aikin jarida:

Yallabai, mene ne takaitaccen tarihinka?
Mu 27 mahaifinmu ya haifa. An haife ni a 1935; shekaruna 79 ke nan. Na shiga firamare a 1943 a Zariya. Na shiga makarantar Midil a 1947. Daga nan na wuce Makarantar Koyar da Kasuwanci ta Kaduna (Kaduna Trade Centre) wacce ta koma Kwalejin Gwamnati da niyyar zama injiniyan gine-gine. Amma rashin lafiya da dogon jinya ya sa shugaban makarantar ya ce in koma middle don sake yin jarrabawa kafin in sake samun damar shigowa makarantar. Na koma bayan na kammala makaranta aka dauke aiki a karkashin gwamnatin Arewa a bangaren kiwon lafiya sannan aka mai da ni ma’aikatar ilimi. Bayan shekara guda aka tura ni Makarantar Horarwa ta Ilori (Ilorin Training College) a matsayin babban akawu. Sannan na je na yi karatun fannin mulki a Cibiyar Mulki wacce ta zama Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
Daga bisani aka ba da umarnin cewa a mai da ma’aikata zuwa kusa da mahaifarsu, sai na nemi a mai da ni Kaduna. Aka ce a gwada murya ta ko za ta dace da shirin ilimantarwa a rediyo a ma’iakatar ilimi. Sai Bature ya ba ni damar shirya shiri. A lokacin ana shirin kafa gidan rediyo da talabijin a Kaduna wato Broadcasting Company of Northern Nigeria (BCNN). Sai na nuna burin na zama dan jarida. Na fara aiki a laburare gun tara faya-fayen garmaho da kaset-kaset a makarantar Technical College, na yi aikin shekara. Ni na kafa bangaren aje kaset-kaset a gidan rediyon na dindindin da ke kan titin Indifenda FRCN, Kaduna. Mataimakina shi ne Alhaji Ladan Kwantagora. Daga baya likkafa ta yi gaba aka mai da ni sutudiyo a matsayin mataimakin mai gabatar da shirye-shirye. Amma kafin nan ina gabatar da shirin ‘Yara manyan gobe.’ Na kuma gabatar da shirye-shirye a kan addini da al’adu da kade-kade.
Shugabana Alhaji Adamu Gumel, ya dauke ni zuwa masallacin Sultan Bello da ke Unguwan Sarki inda muka nemi izininsa don daukar tafsirin Sheikh Abubakar Gumi don sawa a rediyo a watan azumi a 1963 da 1964, sannan ya yarje mana, muka musanya “Wa’azin Musulunci’’ da “Tafsir.’’ Daga minti talatin zuwa awa guda. Yayin da Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya lura cewa awa guda ne ake sawa a rediyo, sai ya rika gudanar da wa’azinsa a awa guda.
Bugu da kari, muka kawo wa mabiya addinin Kirista nasu, wato “Waazin Kirista” da “Wakokin Addinin Kirista” da “Wa’azin tsakiyar mako.” A bangaren al’adu kuwa, na fara rubuta wasannin kwaikwayo da gayyatar makada da mawaka don a dauke su a rediyo da talabijin. Na ba ilimantarwa da fadakaraw da shakatawa muhimmanci don a zauna cikin lumana.
Ko za mu san wani abu game da mahaifinka?
Mahaifina sunansa Alhaji Muhammadu Ladan, marigayi dan Iyan Zazzau wanda na gaje shi. Ya yi karatu a Zariya da Katsina. Ya zama akawu sannan ya yi aikin fassara a gwamnatin Jihar Arewa. Ya je Ingila ya yi karatu sannan ya koyar da Hausa a Jami’ar Cambridge, kafin ya fara aikin rediyo a NBC. Wani Bature mai suna Mista Leslie ne kwanturola na yankin Arewa. Mahaifina ya karbi aikinsa. An karrama shi da lambar yabo ta kasa (MON).
Sannan bayan na gaje shi, kuma dana mai suna, Abubakar Yusuf Ladan ya gaje ni inda yake aiki a gidan Rediyon Tarayya na Kaduna
Su wane ne abokan aikinka?
Mai Shari’a Yusuf Ibrahim da marigayi dan Galadiman Zazzau da Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Alhaji Gidado Idris.
Yaya aka yi ka koma gidan rediyon jiha daga na tarayya?
Ina Mataiamakin Darakta a FRCN aka kirkiro Jihar Katsina daga Jihar Kaduna, sai Babban Manajan Gidan Rediyon Jihar Kaduna (KSBC) Alhaji Aminu Abdullahi ya koma Katsina. Ni kuma aka nemi in cike wannan kafa a matsayin aro daga Gwamnatin Tarayya. Ban taba tsammanin zan bar FRCN ba. Bayan shekara guda, sai na fahimci ma’aikata ba su da kula da aiki saboda ba a kyautata musu. Ana yi musu lakabi da ‘Gidan Rediyon ’Yan doya.’ Sai na kyautata musu ta inganta albashinsu da alawus-alawus.
Lokacin da na fara aiki suna tashi daga gidan rediyon da ke kusa da kasuwa zuwa gidan Muhammadu Ladan da ke layin Wurno Unguwan Sarki, na karfafa wa ma’aikata su rika kula da aikinsu.
Mene ne abin da ba za ka manta ba?
Abin da ba zan manta ba, shi ne kokarin kara yawan harsunan da ake amfani da su a KSBC (KSMC a yanzu). Da batun ya yi zafi sai na je na samu Gwamna dangiwa Umar na ce masa a bar Turanci da Hausa kawai a matsayin harsuna da za a rika yin amfani da su. Domin a lokacin ana ta kurarin sai an kara yawan harsuna. Ni kuma na ga wanne za a dauka, wane za a bari? Don kusan mutanen jihar na jin Turanci ko Hausa, inda Gwamna ya amince.
Me ya sa aka sa wa gidan sunan mahaifinka Muhammadu Ladan?
Don wadanda suka kambama aikin rediyo an fara mantawa da su. Sai hukumar gudanarwa ta amince. Don mahaifina ne babban kwanturola na farko a Arewa. Gwamna Tanko Ayuba ya amince. Sannan wanda aka baro a bakin kasuwar gari aka sauya masa suna, amma ba a yi amfani da sunana ba don ba a makala a allo ba.
Yaushe ka yi ritaya daga aiki?
Na yi ritaya don kashin kaina a 1981.
Su wane ne manyanka a lokacin?
Mista Lesli da Alhaji Adamu Gumel da Alhaji Sani Kwantagora mai kula da shirye-shirye kafin ya koma talabijin. Abba Zoru shugaban sashen Rediyo. Saka Aleshinlowe ne shugaban sashin labaru. Alhaji Balarabe Musa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna shi ne akanta kuma sakataren kamfani. Kuma abokina ne don tare muka yi makaranta.
Su wane ne tsararrakinka?
Ibrahim Ahmad da Yaya Abubakar da Lawal Yusuf Saulawa da Hassan Suleiman da Khalifa Baba Ahmed da Abubakar Abdussalami da Bashir Sama’ila Ahmed da Halilu Ahmed Getso da Abba Gwadabe da sauransu.
Wace shawara za ka ba ’yan jarida a yanzu?
Aikin jarida (musamman) na rediyo shi ne gada tsakanin gwammnati da jama’a. Don rediyo ne ke fadakar da jama’a. Sannan mutane za su iya zuwa gidan rediyo don bayyana ra’ayinsu. Sannan ya dace ’yan jarida su zamo masu gaskiya da rikon amana. Kada su yi aiki domin son kudi, sai don ciyar da al’umma gaba.