Da mai Hajji ya shiga Makka, ya isa masaukinsa, ya sauke kayansa, ya ci abinci, to, ba abin da zai yi kuma sai ya tasar wa Dakin Ka’aba haikan don ya yi Dawaful-Kudumi, wato Dawafin Sauka a Makka. Hukuncin wannan Dawafi wajibi ne, don haka mutum zai yi hadaya idan ya bar shi. Idan mutum ya isa Masallacin Ka’aba an so a gare shi ya shiga Masallacin ta kofarsa wadda a ke kira Babus-Salami. To, ga yadda Mai Hajji zai yi wannan Dawafi:
Tun farko sai ya yi alwala, ya kudirta niyyar Dawafi, sa’an nan ya je kusurwar Ka’aba wadda ake kira Rukunul Hajirul Aswad, wato inda Hajrul Aswad yake. Shi Hajrul Aswad wani bakin dutse ne, shi ne alama ta masomin Dawafi, kuma sai an kawo gare shi ne sa’an nan kewayo daya ke cika, idan ya isa ga wannan kusuwar, sai ya sumbanci Hajrul Aswad da bakinsa, ya kuma ce “Allahu Akbar!” A lokacin da ya ke yin sumbantar nan. Ba zai tsotsi dutsen nan ba, a’a, lebbansa kadai zai dora a bisa gare shi, sa’an nan ya dauke bakinsa. Don yawan jama’a ga misali, to, sai ya tabo shi da hannu, kana ya sumbanci hannun. Idan tabo dutsen da hannu ya yi wuya, sai ya tabo shi da sanda, sa’an nan ya sumbanci kan sandar. Idan har wayau bai samu ikon tabo dutsen nan ba ko da da sanda, to sai ya hakura, shi ke nan ita wannan sumbantar ta wannan kewayo ta fadi gare shi. Ba zai yi nuni da hannu daga nesa ba. Amma duk da haka nan, kafin ya fara kewayon nan, sai ya fuskanci shi Hajrul Aswadun ya ce, Allahu Akbar! Sau daya. Wato ita fuskantar ta tsaya a matsayin sumbata ke nan.
Da mutum ya kare sumbantar Hajrul Aswad, sai ya mike tsaye tsam, ya ja baya-baya kadan, ya sa Dakin Ka’aba a hagunsa, sa’an nan ya fara kewayowa. Amfanin ja da baya-bayan nan shi ne, don a wurin kare kewayo mutum ya tabbata, cewa ya yi wa Dakin nan hadaddiyar zagayowa. A yayin da mutum yake yin kewayon, idan ya kawo ga Rukunul-Yamani zai tabo shi da baki, A lokacin da ya kawo ga Hajrul-Aswad, ya kare kewayo guda cikakke ke nan. Mutum zai kewayo Dakin Ka’aban nan kamar yadda aka siffanta har sau bakwai. Wato zai sumbanci Hajrul-Aswad a farkon kowane kewayowa; haka kuma zai taba Rukunul-Yamani da hannunsa, sa’an nan ya sumbanci hannun. A wurin Dawaful-Kudumi kadai, a kewayo ukun farko, namiji zai yi su da sassarfa, a sauran ragowar hudun kuwa zai yi tafiya ce irin ta al’ada. Mace ba za ta yi sassarfa ba. Da kare Dawafi a kewayowa na bakwai, mutum zai rungumi Multazam don yin addu’a ta alheri. Multazam shi ne bangon Ka’aba. Haka kuma duk lokacin da mutum yake yin kewayon nan na Ka’aba. Addu’a ce kadai yake ta yi, yana rokon Allah abin da yake so na Alheri, kuma a cikin harshen da ya ga dama. Wannan ayar ta dace kwarai a rika karanta ta:
“Rabbana atina fid dunya hasanatan, wa fil akhirati hasanatan, wa kina azaban nar.”
Ma’ana: “Ya Ubangijimmu! Ka yi mana baiwa da kyakkyawan abu a duniya da Lahira. Kuma Ka kiyaye mu daga azabar wuta.”
A lokacin kewayon Ka’aba, mutum zai shigar da Shazirwan da Hijiru Isma’il a cikin kewayonsa. Hijiru Isma’il wani dan gajeren wuri ne a tsakanin Rukunul-Iraki da Rukunush-Shami. Shazirwan kuwa kamar dan dakali ne manne a kewayen Ka’aba.
Mutum idan zai koya wa almajirai yadda ake yin Dawafi yana da kyau ya samu daki mai kusurwa hudu ya kwatanta musu.
Da kare Dawafi, kewayo bakwai, sai mutum ya je wurin Makamu Ibrahim, ya yi Sallah raka’a biyu. Makamu Ibrahim wuri ne a cikin Masallacin kusa da inda ake Dawafi. Hukuncin yin Sallah a nan wajibi ne. Idan mutum ya manta da yin ta har lokaci ya yi tsawo ko kuwa har ya dawo garinsu, to, zai rama, sa’an nan kuma zai yi hadaya idan ya bar ta ce, daga Dawafi na wajibi ko farilla. Da kare Sallah a Makamu Ibrahim, sai mutum ya je ya sumbanci Hajrul Aswad sa’an nan ya je ya sha ruwan Zamzam. Zamzam wata rijiya ce mai asali da ke cikin Masallacin, ya tasar wa Safa don yin Sa’ayi. An so ya bar Masallacin ta kofarsa da ake kira Babus-Safa.
To amma kafin mu shiga Sa’ayi, yana da kyau mu zana wajibai da sunnoni da mustahabbai na Dawafi.
Wajiban Dawafi shida ne su ne:
- Sharudda irin na Sallah game da tsarkin jiki da na tufa da alwala da rufe al’aura. Idan alwalar mutum ta karye a tsakanin yin Dawafi, sai ya yanke shi, ya sabunta alwala, kana ya somo Dawafin tun daga farko. Ya halatta mutum ya yi magana a lokacin yin Dawafi, amma fa sai magana mai kyau kadai aka halatta.
- Dawafi ya zamo a cikin Masallacin Ka’aba, wato ba daga wajen Masallacin ba.
- Mutum ya sanya Ka’aba ta hagu a lokacin kewayo.
- Kewayon Dakin Ka’aba har sau bakwai
- Jerantawar aikin Dawafi. Wato ba zai yi dakatawar banza ba a tsakanin kewayo da wani kewayo mai bin sa. Idan mutum ya manta wani kewayo, daya ko abin da ya fi daya yawa, idan ya tuna tun lokacin bai yi tsawo ba, kuma alwalarsa ba ta karye ba, to sai ya dawo ya aikata abin da ya manta kadai. Amma idan alwala ta rigaya ta karye, to, shi wancan Dawafin ya baci dungum, sai ya rama shi.
- Wajibi na shida shi ne yin Sallah raka’a biyu a Makama Ibrahim bayan kare Dawafi.
Sunnonin Dawafi hudu ne su ne:
- Yin sassarfa a cikin shudi uku na farko. Sassarfa ita ce abin da ta dara tafiya sauri amma ba ta kai gudu ba. Namiji kadai zai yi ta. Idan mutum ya bar yin ta, babu laifi a kansa kuma a cikin Dawaful-Kudumi kadai ake yin ta, ban da Dawaful-Ifala da na nafila.
- Yin addu’a a lokacin Dawafi. Ba a kayyade abin da mutum zai rika fada ba don addu’ar
- Sumbantar Hajrul Aswad cikin kewayo daya na farko kadai.
- Sumbantar Rukunul-Yamani a cikin kewayo daya na farko kadai.
Mustahabban Dawafi hudu ne, su ne:
- Sumbantar Hajrul Aswad a farkon kowane kewayo ban da kewayon farko, gami da fadar Allahu Akbar!
- Sumbantar Rukunul-Yamani a farkon kowane kewayo ban da kewayon farko.
- Mutum ya kusanci Ka’aba idan namiji ne a lokacin yin Dawafi, mace kuwa ta dan nisance ta.
- Yin addu’a a Multazam.
Fadakarwa: shi Dawaful-kudumi ba ya cikin rukunnai na (Farilla) hudun nan na aikin Hajji. Shi wajibi ne kawai. Ihrami shi ne Rukuni na farko, sa’an nan Sa’ayi Rukuni na biyu.
Rukuni na biyu (Sa’ayi)
Sa’ayi shi ne tafiya a tsakanin Safa da Marwa. Yin Sa’ayi a Hajji farilla ne. Don haka idan mutum ya bar shi, Hajjinsa ya baci. Ga yadda mutum zai yi shi:
Mutum zai yi alwala, ya kudirta niyyar yin Sa’ayi, ya je wurin Dutsen Safa ya tsaya, ya yi addua’a tukuna, sa’an nan ya fara tafiya, ya taso wa Dutsen Marwa. Namiji zai yi sassarfa idan ya kawo ga kwarin Badanul-Masili, har ya wuce shi. Mace ba za ta yi wannan sassarfa ba. Ita sassarfar nan a lokacin tafiyarsa zuwa Marwa kadai zai yi ta, ban da a lokacin dawowarsa Safa. A wani kauli, wato wani ra’ayi wannan sassarfar. Idan ya isa Marwa, sai ya tsaya a kanta, ya yi addu’a. Sa’an nan kuma ya juyo zuwa Safa. Zai yi wannan tafiya daya ke nan, dawowa daga Marwa zuwa Safa kuma wata tafiya daya. Wato ka ga da isa Marwa ke nan zai kare shudin nan na bakwai. Wato dai zai tsaya a kan Safa sau hudu domin ya addau’a, haka kuma zai tsaya sau hudu a kan Marwa domin yin addua’a. Zai yi addu’ar da ya ga dama ta alheri, game da duniya ko Lahira ko duka biyu.
Wajibi ne mutum ya kudirta niyyar yin Sa’ayi; kuma wajibi ne ya zamo yana da alwala da tsarkin jiki da na tufa da suturar al’aura. kuma wajibi ne Sa’ayi ya zamo an yi shi bayan wani Dawafi ingantacce. Kowane irin Dawafi ne aka yi ya isa Dawafin farilla ne ko na wajibi ko na nafila. Kuma wajibi ne a cika adadin tafiyar nan ta Sa’ayi har sau bakwai. Wajibi ne kuma tafiyoyin nan bakwai su zamo a jere, suna bin juna, babu dakatawa a tsakaninsu. Idan alwalar mutum ta karye a tsakanin yin Sa’ayi, sai ya sabunta alwala, ya komo ya ci gaba da Sa’ayinsa. Wato ya yi gini a kan tafiyoyin da ya riga ya yi. Wajibi ne kuma a somo tafiya daga Safa. Wajibi ne ga mai iya tafiya ya yi Sa’ayi a kasa a kan kafafunsa.
Sunna ce ga namiji ya yi sassarfa a Badanul Masili. Sunna ce ga namiji ya taka saman Safa da na Marwa don yin addu’a. Haka kuma yake Sunna ga mace ta taka saman duwatsun nan idan wurin babu turmutsitsin mutane a kansu a lokacin yin addu’a a kan Safa da Marwa Sunna ce.
Fadakarwa: Duk lokacin da aka tada Sallah ta farilla a Masallacin Ka’aba, to, mai yin Dawafi ko Sa’ayi, zai dakata da abin da yake ciki, don ya bi liman, ya yi koyi da shi a cikin wannan Sallar.
Da mai Hajji ya kare Sa’ayi sai kuma ya koma masaukinsa, ya dakata, ya saurari zuwan ranar takwas ga Zul-Hajji. Wato ranar Tarwiyya ke nan.