✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ahmed Musa ya raba wa talakawa shinkafa

Rahotannin da suka fito daga garin Jos sun ce shahararren dan kwallon Najeriyar nan da yanzu haka ya canja sheka zuwa kulob din Leicester City…

Rahotannin da suka fito daga garin Jos sun ce shahararren dan kwallon Najeriyar nan da yanzu haka ya canja sheka zuwa kulob din Leicester City na Ingila Ahmed Musa ya raba kayayyakin abinci ga wadansu talakawa a katafaren gidansa da ke garin Jos a karshen makon jiya.
Idan za a tuna, dan kwallon yana daga cikin wadanda sabon kocin Super Eagles Gernot Rohr ya gayyato wadanda suka fafata da kasar Tanzaniya a garin Uyo na Jihar Akwa Ibom a ranar Asabar da ta gabata.
Rahoto ya nuna bayan Ahmed Musa ya ziyarci gidansa da ke garin Jos ne sai ya yi odar buhunan  shinkafa inda shi da kansa ya rika raba wa talakawa don saukaka musu halin kuncin rayuwa da suke fuskanta a halin yanzu.
dan kwallon ya nuna ya yi haka ne don tausaya wa mabukata ganin cewa farashin kayayyakin masarufi sun yi tashin gwauron zabo musamman a wannan lokaci da ake hannu-baka-hannu kwarya.
Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun yi murna da wannan taimako da dan kwallon ya yi musu, inda suka yi masa addu’ar Allah Ya kara girma da daukaka.