Kyaftin din tawagar Super Eagles ta Najeriya, Ahmed Musa, ya sanar da komawa Turkiyya domin ci gaba da taka leda a wata kungiya mau suna Fatih Karagumruk.
Dan wasan ya bayyana hakan cikin wasu sakonnni da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta da yammacin Alhamis.
Tsohon dan wasan na kungiyar Leicester City da a halin yanzu yake buga wa Kano Pillars wasanni, ya jima yana laluben inda zai koma a ketare tun bayan rabuwa da kungiyar AlNassr da ke kasar Saudiyya.
Sabon Kulob din da ya koma ya wallafa hoton dan wasan tare da farin cikin kulla yarjejeniya da dan wasan.
Rabuwa da AlNassr
Bayan kwashe shekaru biyu yana fafatawa a gasar kwallpn kafar Saudiyya, Ahmed Musa ya kawo karshen zamansa da kungiyar AlNassr FC wadda ake yi wa lakabi da Najd Knight.
Kungiyar wadda ta lashe gasar kwararru ta Saudiyya har sau takwas, da kanta ta bayyana hakan cikin wani sako da ta wallafa shafina na Twitter a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoban bara.
Kungiyar ta yi wa dan wasan fatan alheri bayan sun raba gari cikin salama.
Cikin sakon da kungiyar ta wallafa na bankwana, ta tattaro tarihi tun daga tarbar da aka yi masa farkon zuwansa tare da kwallayen ya jefa da yadda yake atisayen motsa jiki na wasu lokutan.