✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Africa Magic da Showmax Za Su Bawa Masu Shirya Finafinai Aiki

Sabbin shirye-shiryen sun hada da na tarihin fitaccen tsohon dan wasan Najeriyan Jay Jay Okocha

Shugaban Sashin kula da Shirye-shiryen tashoshin Talabijin din Kamfanin MultiChoice na Yammacin Afirka, Busola Tejumola, ya ce Tashoshin Africa Magic da Showmax za su bawa masu shirya fina-finai 30 aiki a 2023.

Tehumola ya shaida wa taron jagororin Showmax da DSTV da masu shirya fina-finai na Afirka cewa masu kallon tashoshin biyu za su samu samun karin sabbin shirye-shirye masu yawa da kuma ragi kan shirye-shiryen nishadi da zarar hakan ta tabbata.

Ya ce sabbin shirye-shirye 30 da za a samar sun hada da na tarihin fitaccen tsohon dan wasan kwallon kafar Najeriyan Jay Jay Okocha da aka yiwa lakabi da Wura.

Taron da aka gaudanar don bikin fina-finan Afirka (AFRIFF) karo na 11th, jarumar kuma furodusar Nollywood, Padita Agu ce ta jagorance shi tare da wasu manyan mambobin kwamitin.