Edita don Allah ina so a mika min sakona gurin iyayen yaran da aka sace a Chibok da sauran dukkanin matan Arewa gaba daya da su zage damtse wajen ganin sun kwato ’yancin ’yan uwansu. Mu kuma za mu taimaka musu da addu’a da kayan aiki. Domin mun ga Gwamnatin Najeriya ta nuna halin ko-in-kula. Talakawa dai babu abin da za mu iya yi sai addu’a, domin mun san Allah Ma-ji roko ne. In Allah Ya yarda, sai kun kubuta, albarkar Annabi da Alkur’ani. Daga Musa Umar dankanjiba, Jihar Katsina, Mazaunin Legas 08142494277.
Sakonnin waya
Haba Tor Tib!
In ka hana fili (kasa) ga Fulani a kasarka to ba ka tunanin talakawanka Tibawa in sun zo kasarmu ga Hausa da Fulani mu ma za mu hana su kasa. Ranka ya dade, hatta haya ma za mu hana su. A rika hangen nesa. Daga Mohammed Sani Garba
Ga APC a Jihar Katsina
Jam’iyar APC Jihar Katsina.Ya kamata ki gaggauta warware rikicin cikin gida da kike fama da shi, domin idon har baki warware wannan rikici ba, To zai yi wuya ki samu nasara a zaben da ke gabatowa. Daga Haruna Muhammad Katsina. 07057491050
PDP na shure-shure
Edita don Allah ka ba ni dama na yi tsokaci dangane da matakin da PDP ta ce za ta dauka cewar za su kai kara kotu akan zaben kananan hukumomin da aka gudanar a Kano hakika PDP tana mantawa ne da irin karfa-karfar da take yi wa talakawa a lokacin zabe; abin da muka zaba daban, abin da suke ba mu daban. Daga Aminu Abdu Baka noma, Sani mai nagge Kano 08099479880.
Ga Mai martaba San Kano
Salam Edita. Don Allah ka ba ni dama na nuna farin cikina da dawowar mai Martaba Sarkin Kano daga kasar waje. Ya fita neman magani, muna yi wa Allah godiya; Allah Ya kara masa lafiya; Allah Ya ba mu zaman lafiya mai dorewa. Daga Muhammad Aminu Baka noma Kano 08069735151.
Godiya ga Idon mikiya
Salam. Edita ina so in yi godiya ga ma’aikatanku da na rediyon bision FM, kan yadda suke wayar da kan jama’a, musamman a shirin ‘Idon Mikiya.’ Muna amfana da ku, Allah Ya yi muku sakayya ta alheri. Daga Muhamamd dan Chiranchi 07056991838.
Jaje ga Kanawa
Ina jajanta wa mutanen Kano game da tashin bom da ya auku. Allah Ya kare gaba. Bayan haka wai me aka mayar da Arewacin Najeriya? Mu ci gaba da rokon Allah Ya tona asirin masu zaluntarmu. Daga Sufiyanu SKK. 08064174416.
Ga ’yan Arewa
Salam ‘’yan Arewa mu ci gaba da addu’a, Allah Ya ba mu zaman lafiya. Daga Muhamman Sanda dan Nijar, Dei-dei, 07056991838.
Ga Aminiyar Aminiya diamond
Edita ka cigito min Aminiyar Aminiya, Aysha Diamond, wadda ma’abuciyar jaridar Aminiya ce daga Gombe. Allah Ya sa a ganta. Daga Aliyu H. Kano 08092516853.
An yi magudi a Kano
Salam. Don Allah Edita ka isar da sakona. Zaben kananan hukumomi da aka yi ranar Asabar din da ta gabata a Kano, an tafka magudi. Kwankwaso adalcin ke nan? Daga Mallam Lawal Shehu Daura 08064932828.
Ga Aminiya
Zuwa ga Aminiya. Ki yi mini tsokaci bisa abin da na fadi. Mu ’yan Jihar Yobe sai abin da Allah Ya yi. Daga Sa’idu AbdulMumini Fika, Jihar Yobe 07063856392.
Haba PDP!
Haba ’yan PDP boko Haram din da kuke yi a Maiduguri bai isheku ba, har sai kun hada da Kano? To Allah Ya fi ku. Daga Rufa’i Maiduguri 08032821884.
Addu’a ga Najeriya
Ya Allah Ka jikanmu, Ya Allah Ka ji tausayinmu; ya Allah Ka ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarmu Najeriya. Kuma Allah Ya kawo mana karshen zubar da jini da hare-haren bama-bamai a Najeriya. Saboda yau a Najeriya babu tsaro sai dai tsoro, don haka muna jajanta wa wadanda suka rasa rayukkansu a jihohin Maiduguri da Yobe da Adamawa da Zamfara da Abuja. Daga Zaidu Bala Kofa Sabuwa Birnin Kebbi, Jihar Kebbin Najeriya. [email protected].
APC maganin barayi
Hakika shawarwarina na bai wa APC forum ta ’yan kishin kasa a Aminiya sun yi tasiri. Domin nag a barayin shanu sun firgita a garuruwanmu na jihar Katsina; na kuma tabbatar ba aikin Shema ba ne. Don haka APC ki bullo da hanyoyin magance satar shanu a jihohin Arewa. Allah Ya ba ku sa’a; ya kawo mana sauyi mai amfani. APC maganin barayin shanu; maganin masu kwashe dukiyar kasa. Daga Ibrahim Runka, kanen danmadamin Kokon Turawa 0805445268.
A farka ’yan Arewa
An gama da mu ’yan Arewa, domin mun yi barci, wanda ba za mu farka ba. Allah ya yi mana jagora. Amin. Daga Usman Mukhtar M. A, D/Tofa Kano 08164234292.
Ina EFCC da ICPC?
Aminiya wai ina hukumar cin hanci da rashawa EFCC da ICPC? Anya suna sane da badakalar da ake yi a kasar nan? Ko dai linzami ya fi karfin bakin kaza? Daga danliti Pillars, Rimin Kebe, Kano 07037874889.
Ga makiyan Najeriya
Makiyan Najeriya, kasar nan za ta yi kyau a karkashin tutar jam’iyyar APC, in sha Allahu. Daga Sani Abdu Beta 07068223015.
Ga ’yan Kala-Balge
Gaisuwa gare ku matasan da suka kashe mahara 200 kun fi sojoji karfin hali. Allah Ya tsare ku. Daga 08156575650.
Ga Gwamna Yero
Wai mai girma gwamna me ka tanadar wa mutanen Jihar Kaduna bayan da ka janye acaba? Shin Gwamna Yero ka yi shirin tanadin aikin yi ga dimbin matasan da ka raba su da hanyar neman abincinsu? Muna fatan gwamna da mukarrabansa za su yi kyakkyawan tunani, musamman a irin wannan lokaci da ake cikin wani hali. Daga Musa na Musa PZ na Ummulkheery 08156572079.