✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adam A. Zango ya saki matarsa ta shida

Safiya Chalawa ita ce matar Adam A. Zango ta shida da ya saka; ’ya’yansa bakwai, kowanne mahaifiyarsa daban, in banda biyu daga cikinsu

A karshe dai shahararren mawaki kuma furodusa a masana’antar finafinai ta Kannywood, Adam A. Zango, ya saki matarsa, Safiya Umar Chalawa.

Jarumin ya sake ta ne shekara hudu bayan aurensu da aka daura a 2019 a Fadar Sarkin Gwandu a Jihar Kebbi.

Da haka ne Safiyya ta zama matarsa ta shida da ya saka a cikin shekaru 17 da suka gabata, daga 2006 zuwa yanzu.

Adam A. Zango, wanda ya yi tashe a Kannywood, yana da ’ya’ya bakwai, kowanne daga cikinsu mahaifiyarsa daban, in banda biyu daga cikinsu.

A kwanakin baya Aminiya ta ruwaito cewa Adam A. Zango na dab da rabuwa da amaryarsa Safiya, wadda aka ji shi a wani bidiyo yana zargin cewa ta zabi kasuwancinta a kansa.

A cewarsa, hakan ne ya sa ba shi da wani zabi face ya hakura da ita, kuma idan ya rabu da ita ba zai kara yin aure.