Kadaden shiga da Birnin Tarayya Abuja ke samarwa na cikin gida a shekara sun fara kaiwa Naira biliyan 200.
Ministan Birnin Tarayya, Muhammed Musa Bello ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi a taron mako-mako na ministoci wanda tawagar sadarwar shugaban kasa ta shirya.
- Gwamna Bala ya sake nada tsohon dan takarar gwamna mukamin Sakataren Gwamnati
- Sarauniyar Ingila Elizabeth II ta cika shekara 70 a kan mulki
Ya ce yanzu haka Abuja ita ce ta biyu a samar da kudaden shiga na cikin gida, kuma tana shirin doke Jihar Legas wacce a yanzu ita ce ta daya a fadin Najerya.
Haka kuma ya ce an ware Naira biliyan daya domin yin kwaskwarima ga babban masallacin Abuja da kuma Coci, don jan hankalin masu yawon bude ido ga birnin.
Haka kuma ya ce gwamnati na yin gyaran fuska ga Sakatariyar Tarayya da Majalisar Dokoki ta Kasa inda za ta sauya fasalin kujerunsu duka.
Dangane da kalubaken tsaro da gine-gine da ba a kammala ba suke kawo wa Abujan, da kuma tsadar haya, da yawan mutane, ya ce gwamnati na nan tana shiri a tsarin da ba zai tashi hankalin al’umma ba.
Kazakika ministan ya ce masu gina gidaje nesa da birni suna tsawwala farashi ma gwamnati za ta yi wani abu akansu.
Ya kuma ce duk da wadannan matsalolin, birnin ne mafi zaman lafiya a Najeriya, domin jami’an tsaro na matukar kokari.
Ya ce, “Misali kalli yadda gidan kasonmu ke cike da ’yan Boko Haram, duk kokarin jami’an tsaronmu ne.
“Yadda suke samun matsuguni da kuma yadda suke sajewa da mutane shi ne abin da na gaza fahimta”, in ji shi.
Sai dai ya koka kan yadda kalubale ya dabaibaye bangaren kotunan manyan laifuka, duba da yadda gidajen gyaran halin birnin ke cike makil.
Haka kuma ya roki Gwamnatin Tarayya da ta dinga kama masu fada a jin da ke karbar belin wadanda ake zargi da aikata babban laifi.