Matsalolin jiki da ma na wajen jikin da dama za su iya taba lafiyar kafa, tun daga saman jiki har kasa, wato tun daga ciwo irin su bugun jini a kwakwalwa har zuwa buguwa ta hadari.
Idan aka samu bugun jini a kwakwalwa kafar bari guda na iya shanyewa ta kasa motsi, a ga an samu nakasa a kafar.
Haka nan ma idan kwayar cutar shan inna ta kama yaro zai iya rasa kafafu duka biyu, a ga sun shanye, a ga nan ma an samu nakasa a kafa.
Idan aka duba sauran kwayoyin cuta da kan shiga kafa su sa ciwo, ka ga ai akwai ciwon kurkunu (wanda aka ce an kawar) wanda kwayar cutar da cunculus take kawowa.
Akwai ciwon tundurmi wanda kwayoyin cutar filarial ko na onchocerca suke kawowa, ka ga kafa ta kumbura suntuntum kamar ta giwa.
Sannan akwai cin ruwa na tsakanin yatsu, wanda shi ma kwayar cutar fungus ke kawo shi.
Haka nan ma kuturta, wadda kwayar cuta ce, takan nakasa kafa ta cinye yatsun.
Sannan idan aka zo maganar sauran cututtukan cikin jikinmu masu iya kawo ciwon kafa, ai ka ga ba za a bar ciwon suga ba, wanda kan sa jijiyoyin kafa su mutu, mutum ya yi ta jin rauni bai ma san yana da raunin ba.
Sai kuma raunin ya zo ya ki warkewa saboda tsananin yawan suga a jiki, abu ya zama gyambo.
Haka nan ma yara masu ciwon sikila sukan iya samun gyambo a kafa su kuma saboda jini ba ya kwaranya a kafar sosai.
Masu hawan jini da ciwon zuciya da kiba, su kuma yawanci ba su da ciwon kafa, sai sun yi ’yar tafiya hanyoyin jini sun fara tottoshewa sai su rika jin wani irin zogi na rike musu kafa, wanda sai sun huta suke saki. Wannan daga motsewar jijiyoyin jini ne.
Haka nan masu kiba na yawan samun ciwon tafin kafa wanda sai sun rage ta yake tafiya.
A ’yan mata kuma, yawan sa matsattsen takalmi sannan idan sinadaran jiki suka yi yawa kamar na calcium ko na gishirin uric acid zai iya kawo ciwon sanyin kashi na gout, wanda kumburi ne da ciwo sosai mai ‘sanyi’ a yatsa.
Haka nan ma wasu kan iya su gaji sinadarai a jikinsu su samu ciwon sanyin kashi na rheumatism, wanda shi kuma ya fi kama gwiwoyin kafa, su kumbura su yi ta ciwo.
Idan ka zo kan tsofaffi kuma, musamman mata, su ma za ka ji haka nan suna yawan korafin ciwon kafa, amma ba kumburi ba komai, wannan ana ganin zaizayewar kashi ke jawo shi.
Sa’annan idan ka zo maganar cizon dabbobi, nan ma za su iya sa mutum ciwon kafa, harbin kunama zai iya sawa, sai dai bai kai na sarar maciji illa ba, wanda shi kuma dafinsa zai iya sanadiyar kafa rko ma mutum gaba daya.
Sannan ina ka bar maganar cizon kare, wanda shi ma yawanci kafa yake ciza, wadda idan ba a dauki mataki ba, zai iya sanadin kafar shi ma, ko ya sa ciwon haushin kare na rabies.
Haka nan mutum zai iya buguwa a hadari ko a wurin wasanni ya samu karaya ko gocewar kashi, ko a samu rauni, kamar yankewa ko kujewa duk za su iya sa ciwon kafa.
Wani lokaci buguwar ko a gadon baya ne, za ta iya shafar kafa.
Wadansu kuma akan zo musu allura, a yi rashin dace allurar ta taba jijiyar laka, kafa ta shanye, shi ke nan an nakasa ta ke nan.
Yawanci wannan ’yan karambanin aikin likita ne ke jawowa ba likita ko nas din kwarai ba. Sannan daga karshe akwai wadanda haka nan aka haife su da larura a kafa.
Wadansu yaran kuma sai sun fara tasawa suke samun ciwon gwame saboda karancin sinadaran bitaman D da calcium.