✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa hudu da bai kamata ka karya su ba a rayuwa (3)

Tare da sallama, kamar yadda muka saba: Assalamu alaikum. Bayan haka, za mu dora ga maudu’in da muka faro makonni biyu da suka gabata.Kamar yadda…

 Zumunci na nufin haxin kai da kyautata wa juna!Tare da sallama, kamar yadda muka saba: Assalamu alaikum. Bayan haka, za mu dora ga maudu’in da muka faro makonni biyu da suka gabata.
Kamar yadda maudu’inmu na sama ya nuna ‘Abubuwa hudu da bai kamata ka karya ba a rayuwa,’ mun riga mun bijirar da bayanai game da abubuwa ko tubala biyu, wato ‘Amana’ da ‘Alkawari.’ A wannan karon kuma za mu dauki tubali na uku, wato ‘Zumunci’ domin mu dan yi tambihi, mu bayyana dalilan da za su sa mu rike zumunci da muhimmanci, sannan mu bayyana illolin da ke tattare da karya ko tsinka igiyar zumunci.
Kafin mu yi nisa, bari na dan bijiro da wani gargadi: A matsayinmu na mutane ‘’yan Adam, mu sani cewa lallai zumunci shi ne tushen rayuwa, shi ne kuma babban jigon yaukaka dadin zama cikin fa’ida da lumana tsakanin kowace al’umma. Don haka, a duk inda muka samu kanmu, to mu yi kokari iyaka karfinmu domin kullawa da jaddada zumunci. Kada mu sake mu tsinka ingiyar zumunci, ko ta me kuma ko don me!
A kowane lokaci, zumunci ne ke haifar da yarda da aminci tsakanin mutane. Zumunci ne ke zama babban tsanin da ke sadar da nasara ga mutum a rayuwarsa, ya Allah a fuskar kasuwanci, aiki ko mulki da dai sauran harkokin yau da kullum na rayuwa. Da zarar mutum bai da abokan zumunci, babu wata harka tasa da zai ji dadin gudanar da ita, domin kuwa kamar yadda Hausawa suka ce, yawan mutane shi ne kasuwa ba tarin runfuna ba. A lokacin da aka ce ba ka da abokan zumunci a harkarka, to kuwa zance ya lalace ke nan, domin kuwa babu yadda za a yi ka tafiyar da al’amari kai kadai zikau.
Idan za mu dauki misali da harkar aure, za mu ga yadda zumunci ke taka muhimmiyar raya wajen dinke al’umma da saita su zuwa ga aikin alheri. A lokacin da zumuncin aure ya hada ka da wata, to kuwa shi ke nan kai da ita kun zama daya. Tun daga kakanninta na farko a tsatsonta har zuwa kan jikan karshe da za ku haifa da ita, kun zama ’yan uwan juna, kun zama aminan juna. Haka kai ma abin yake a bangarenta, tun daga kakanninka na farko zuwa jikanku na karshe, duk kun zama daya. Wannan shi ne abin da ake kira ’yan uwantaka ko dangantaka ko zumunci mai girma.
A nan, madamar kana son zama cikin lafiya da kwanciyar hankali, madamar kana son samun nasara da fa’ida a cikin al’amuranka da zamantakewarka na rayuwa, to ya zama wajibi ka karfafa dukkan matakan kyautata zumuncinka da matarka da iyalanta da tsatsonta gaba daya. Haka ita ma za ta yi zuwa gare ka da danginka da ’yan uwanka. Idan aka samu haka, shi ke nan duniya ta yi daidai kuma ta yi dadi.
A batun zumunci ta fuskar aurataya, ya zama wajibi ka zama kambamau, watau wanda ya hada kowa da kowa a zumuncin. Misali, ba za ka samu fa’ida ba idan ka ce za ka ware wasu ka yi zumunci da su, sannan ka ware wasu ka ce babu ruwanka da su. A nan ina magana ne a kan batun zumuncin aure. Ba zai yiwu ka ce kai dangin uwar matarka ne kadai naka ba, a’a, dole sai ka hada da na babanta. Haka ita ma, babu yadda za ta ce za ta yi zumunci ne kadai da dangin iyayen miji na bangaren uba, ta banzatar da dangin iyayen miji na bangaren uwa. Idan ta yi haka, kamar a ce mota ce mai kafa biyu, ba za ta tafi daidai ba yadda ake bukata.
Idan ka fito waje kuwa, duk wanda Allah Ya hada ka da shi bisa wata harka ta rayuwa, to ya zama abokin zumuntarka. Misali a nan shi ne, kamar makwabcinka ko abokinka na wurin aiki ko na wurin sana’a da sauransu. Yi kokari ka ga cewa kun gudanar da harkokinku bisa gaskiya da adalci da amana. Yi kokari ka kare mutuncinsa da kimarsa da darajarsa. Idan ka yi haka, babu shakka zumuncinku zai dore kuma zai zama mai fa’ida da amfani.
Wani abin lura kuma shi ne, a duk lokacin da alaka ta hada ka da wani, koda ba dan uwanka ba ne na jini, to idan kun tashi rabuwa, ka yi kokari ku rabu cikin lumana. Kada ka sake ku yi rabuwar dutse hannun riga, ma’ana kada ku rabu cikin fushi ko da fada. Idan kuka yi haka, to duk ranar da za ku sake haduwa a wani wuri, haduwar ba za ta yi fa’ida ba. Kuma kada ku manta cewa duniya fadi ke gare ta, ba ku san rana da wurin da za ku sake haduwa da juna ba.
Zumunci dai babban al’amari ne kuma shi ne babban sinadarin da ke dinke al’umma su zauna lafiya da juna, kamar kuma yadda yake wanzar da ci gaba da bunkasar al’umma. Mu sada zumunci, mu karfafa shi, kada mu tsinka shi!
Za mu ci gaba