A takaitaccen bayani da ya gabata, lallai mun san irin hakkin da maraya yake da shi da kuma wajibcin tsayawa tsayin-daka a kan a kula da dukiyarsa; sannan da bayanin munzalin da maraya zai kai sannan a danka masa dukiyarsa; sannan da bayanin cewa wannan aiki ba karamin matsayi yake da shi a wurin Allah ba.
Wannan kuma zai dada fayyace mana yadda Musulunci, a kullum, yake kulawa da masu rauni. Sannan ga shi yadda bayani ya gabata, wadanda suka fi shan wahala su ne mata da kananan yara; kuma ga yadda Allah Ya yi bayani a kan dukkan mai cin dukiyar maraya da zalunci, to wuta yake ci ma cikinsa. Allah Ya tsare mu kuma dukkan wadanda suke kula da marayun da ke hannunsu, ya Allah Ka taimaka musu wurin sauke wannan nauyi, kuma Ya Allah ladar da Kake baiwa wadanda suke kulawa da marayu, Ka tabbatar mana, mu da su baki daya. Amin.
Juya Baya A Lokacin Yaki
Ja-Da-Baya ko Juya Baya A Lokacin Yaki (Lokacin Gumurzu): Wannan shi ne abu na shida ciki abubuwa bakwai da Ma’aikin Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya lissafa cikin abubuwan da suke halakar da wanda yake ta’ammuli da su.
Jihadi wani al’amari ne da Musulunci ya shar’anta shi, ya kuma tsara shi kamar yadda ya tsara rayuwar bil’adama ta duniya da kuma ta lahira. Ayoyi na Alkur’ani da ingantattun Hadisan Ma’aikin Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, duk sun zayyana yadda jihadi yake. Haka nan kuma malamai sun zayyana yadda yaki yake domin habaka addinin Allah. Kuma kamar sauran al’amura, sai mutum ya yi kamar yadda aka shar’anta sannan zai sami ladar shi.
Yaki domin habaka addinin Allah shi ne kololuwar Musulunci, kamar yadda Ma’aikin Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya bayyana a hadisin Mu’az. Kuma kamar yadda Allah Madaukakin Sarki ya bayyana a cikin Alkur’ani cewa: ‘’An wajabta muku yaki alhalin bakwa sonsa.’’ Bakara, aya ta 216.
A wannan dogon hadisi da muke bayani a kan shi, Ma’aikin Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya lissafa juyawa da nufin gudu, yana daga cikin abubuwa masu halakarwa domin kamar wannan juyawar da mayaki ya yi yana nufin a murkushe Musulunci ke nan.
Amma juyawar da za ta laifi sai idan yawan musulmai daidai ne da na kafirai, ko kuma su wadanda ba musulman ba sun ninka musulmai ribi biyu, amma idan yawan wadanda ba musulmai ya ninka yawan musulmai sama da sau biyu, to a wannan lokaci babu laifi idan musulmi ya juya da baya, kamar yadda ayar Suratul Anfal ta yi nuni: ‘’Ayanzu Allah Ya sawwaka muku, kuma Ya bayyanar da cewa a cikinku akwai masu rauni, idan an sami mutane dari daga cikinku masu hakuri, za su rinjayi mutane dari biyu (daga cikinsu), in kuma an sami mutane dubu daga cikinku, za su rinjayi dubu biyu (daga cikinsu) da izinin Allah, Allah Yana tare da masu hakuri”. Aya ta 66.
Ma’aikin Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana cewa, ‘’Kada ku yi fatar haduwa da abokan gaba, ku roki Allah zaman lafiya, idan kuma har kuka hadu da su, to ku tabbata. Ku sani aljannah tana karkashin inuwar takobi’’.
Ya Allah, muna rokon Ka zaunar da mu lafiya, kuma Ka dawo wa Musulunci izzarsa da kimarsa da darajarsa.
Wannan ya nuna yadda Musulunci bai yarda da juyawa da baya ba a lokacin da aka yi fito-na-fito, kuma mu sani, a nan ba wai ana bayani ne a kan abin da ya shafi hukunce-hukuncen yaki ba ne (Jihadi). Wannan wurinsa daban, malamai sun fayyace shi da yadda ya karka su da matsayin kowane kaso daga cikinsu, amma a nan an yi bayani ne a kan abin da ya shafi tserewa ne daga fagen fama.
Ya Allah, Ka tsare mu ka tsare mana rayukanmu da imaninmu. Amin.