✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa bakwai masu halakarwa (7)

(2) Sharadi Na Biyu, Wayau: Ko da yaron da kake kula da dukiyarsa ya balaga, to bai halatta ka ba shi dukiyar ba sai ka…

(2) Sharadi Na Biyu, Wayau: Ko da yaron da kake kula da dukiyarsa ya balaga, to bai halatta ka ba shi dukiyar ba sai ka jarraba hankalinsa da dabararsa da wayonsa. Idan ya natsu, sai ka danka masa, idan kuwa bai natsu ba, to bai halatta ka ba shi ba.

Wadannan sharudda guda biyu su ne aya ta 6 cikin Suratun Nisa’i ta yi bayani. Allah Madaukakin sarki Yana cewa: “Kuma ku jarraba marayu, har idan suka isa aure, to idan kun tabbatar da wayonsu, sai ku ba su dukiyoyinsu. Kada ku ci ta (dukiyar) da barna da gaggawa kafin su girma (komai ya kare). Duk wanda yake mawadaci ne, to ya kame, wanda ko fakiri ne (marashi ne) to ya ci gwargwadon wahalarsa. Idan za ku danka musu (dukiyar), to ku kafa musu shaida, lallai Allah Ya isa Mai lissafi a kan komai”.
Wannan babbar aya ce a kan abin da ya shafi kulawa da dukiyar maraya a tsari mai cike da adalci da tausayawa da ba kowa hakkinsa.
Da farko dai ayar ta yi nuni da a dinga jarraba su marayun, har idan aka ga sun cika wadancan sharudda biyu, sai a ba su dukiyarsu. Sannan ayar ta ja kunnen masu kula da dukiyar da kada su tasa ta a gaba da ci ham-ham, kafin yara su girma babu komai. Sai ayar ta bayyana hakkin mai kula da dukiyar, idan shi mai kula da dukiyar maraya da ma mawadaci ne yana da harkokinshi, to ya ci gaba da kulawa, amma ya kame daga cin wani abu na dukiyar. Idan ko talaka ke kulawa da dukiyar marayan, ta shagaltar da shi daga nashi fadi-tashin, to ya dauki gwargwadon wahalarsa. Ma’ana, in da wani ka dauka aiki yake kula ma da dukiyarka, nawa za ka ba shi, to abin da ka san za ka ba shi, haka za ka dauka.
Sannan ayar ta nuna mana cewa idan lokacin damka wa maraya dukiyarsa ya yi, kada ku kunshe kanku a daki, a’a, ku kafa shaidu. To ke nan ma a lokacin da za ka karbi dukiyar maraya, ka tabbatar an sa shaidu kuma a rubuta adadin abin da ka rike. Kada ka yarda a ce, ‘ai ba sai an rubuta ba, ba danka ba ne’? Sau da yawa mutum ba zai raka ka ba, ya ce dare ya yi ma. Wasu su za su zugo maryun, bayan sun girma, a ce ‘babanku ya bar muku abu kaza da abu kaza’, a nemi a hada ka fada da ‘ya’yan kanenka ko yayanka. Allah Ya sawwake!
Sannan wurin shaidun, ba lallai ba ne a ce sai dattijai, a hada da matasa, wadanda suke da wayau. Allah ne dai kadai Ya san gawar fari.
Sai Allah Ya rufe ayar da: ‘Ya isa ya zama mai lissafi’. Wannan yana nuna mana cewa a tsaya a yi lissafi mai kyau lokacin karba da kuma lokacin bayarwa. Za ka lissafa duk abin da kake kashe wa marayan da ke hannunka, kamar kudin makaranta; kudin koyon sana’a; domin za ka tsaya ne ka kula da tarbiyyarsa. Lokacin muzurai, a yi mishi muzurai; lokacin fada, a yi mishi fada; in ya yi abin duka, a doke shi, amma ba duka mai tsanani ba. Domin sai an runtse ido ake shan magani, musamman a irin wannan lokaci da tarbiyya ta sukurkuce. Ka sa shi makarantar Islamiyyah da ta boko da koyon sana’a, sai ka ga ya girma ya zama natsattsen mutum kamili. Ga kuma irin wannan dimbin lada da ka samu, domin duk wadannan al’amurra da kake wa wannan maraya kana da lada ta musamman a wurin Allah.
Ayoyin Alkur’ani sun zo da bayanin kada ku yi kusa da dukiyar maraya sai da abin da yake shi ne mafi kyau. Saboda yadda ayoyi suke magana a kan dukiyar maraya, sai da ya kai wasu sun nemi su ware dukiyarsu da ta maraya, ba tare da sun hada ba, ko da jinsinsu guda, kamar dabbobi; kayan gona; kudi da sauransu.
A Suratul Bakara aya ta 220, Allah Madaukakin sarki yana cewa: “Kuma suna tambayarka dangane da marayu, ka ce: Kyautata musu shi ne daidai, har idan kuka hada dukiyarku da tasu ai ‘yan uwanku ne (ba komai), Allah Ya san mabarnaci kuma Ya san mai gyara”.
Kuma ya kamata al’umma su tsaya su yi karatun ta-natsu a kan marayu! Bai gagara mutum shi ma ya mutu ya bar nashi yaran kanana, ai shi ma ba zai so abin da ya bar musu wani ya yi wandaka da shi ba.
Saboda haka lissafa cin dukiyar maraya ba-gaira-ba-sabab da Ma’aikin Allah ya lissafa shi cikin abubuwa bakwai masu halakarwa, ba karamin tashin hankali ba ne.