✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa 6 da za a kiyaye don magance jemewar fata

Akwai abubuwa da dama wadanda suka kamata a yi la’akari da su domin magance jemewar fatar jiki da kuma ta fuska. Wadannan abubuwa kuwa jama’a…

Akwai abubuwa da dama wadanda suka kamata a yi la’akari da su domin magance jemewar fatar jiki da kuma ta fuska. Wadannan abubuwa kuwa jama’a da yawa ba su san da su ba. Don haka ne a wannan makon za mu yi muku bayanin wadannan abubuwa 6 don ku kiyaye su.
Fatar jiki na da matukar muhimmanci a jiki, don haka, ya kamata mu kula da ita. Fata mai kyawu na kara fitowa da mace, ta gyara mata kwalliyarta, wani lokaci ma ba sai ta yi kwalliyar ba idan tana da fata mai kyawu.
A fahimta:
·         Yawan goge fuska da ruwan goge fuska (cleanser) na sanya jemewar fatar fuska. Idan ana da fata mai gautsi, to ya kamata a wanke fuska da sabulu da ruwa, kafin a kwanta barci ba tare da an sanya wa fuska ‘cleanser’ ba.

·         Yawan durza fuska da karfi idan an zo wanke ta na janyo fesowar kuraje a fuska da kuma sanya fata jemewa. Fata na son a lallaba ta. Saboda haka, ya kamata a rika lailaya fata kamar ta jinjiri, ko da ana wanke ta da sabulu ne.
·         Amfani da mayuka masu dauke da sinadarin (sunscreen) na da muhimmanci sosai, domin wadannan mayukan na kare fuska daga kunar rana. Don haka dole a samu man da ke dauke da irin wannan sinadarin domin magance jemewar fata.
·         Yawan kwanciya a kan hannu a benci, musamman ga ma’aikata na sanya fata ta yi sako-sako. Yin hakan na sanya fata jemewa.
·          Yawan amfani da tsinken shan lemu (straw) na sa fatar baki ta sake. Domin bakin zai kasance kullum cikin tsotsa. Sai a ga fatar bakin ta fara fitar da layuka, a karshe hakan ya haifar da jemewar fatar baki.
·         Kada a manta da motsa jiki, domin hakan na taimaka wa jinin jikinmu zagaya jiki, ba tare da takura ba. Idan kuwa jinin jiki na zagaya cikin sauki, to hakan zai sa fata ta yi sumul. Yana da kyau a rika motsa jiki kamar na minti 30 a kullum domin samun lafiyar jiki.