✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimman abubuwa 10 game da sabon shugaban EFCC

Zai zama Shugaban EFCC mafi karancin shekaru kuma mutum na Farko daga Arewa ta Yamma.

Yayin da Shugaba Buhari ya ayyana Abdulrasheed Bawa domin zama sabon Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC), Aminiya ta tattaro muhimman abubuwa 10 da ya kama ta ku sani game da shi.

  1. Abdulrasheed Bawa mai shekara 40 haifaffen garin Jega a Jihar Kebbi shi ne mafi karancin shekaru a jerin shugabannin Hukumar tun da aka kafa ta.
  2. Zai zama Shugaban EFCC na Farko daga yankin Arewa Maso Yamma kuma a halin yanzu shi ne Babban Jami’in Ofishin EFCC a Legas, ofishin mafi muhimmanci a hukumar bayan Hedikwatarta.
  3. Ya yi aiki da daukacin shugabannin Hukumar da suka gabace shi, tun daga shugabnanta na farko, Malam Nuhu Ribadu wanda ya dauke shi aiki tare da sauran fararen hula rukunin farko a 2005.
  4. Abdulrasheed Bawa ya fara aiki ne a ofishin hukumar da ke Legas, inda daga nan aka tura shi ya yi aiki a Abuja da Fatakwal.
  5. Ya karanci fannin Tsimi ta Tanadi a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato inda ya samu Digirinsa na farko a 2001 sannan ya yi Babban Digiri a fannin Huldar Diflomasiya a 2011.
  6. A 2016 Abdulrasheed Bawa ya samu karin girma zuwa matsayin Mataimakin Babban Sufirtanda Mai Binciken Kwakwaf.
  7. Ya jagoranci wasu muhimman binciken laifukan kudi, ciki har da badakalar kudin mai da ake zargin tsohuwar Ministar Kudi, Diezani Allison-Madueke; binciken tsohon Gwamnan Neja Mu’azu Babangida Aliyu; badakalar musayar mai mai cike da sarkakiya; da kuma badakalar tallafin mai daga 2012 zuwa 2015.
  8. Ya jagoranci Ofisohin Hukumar da ke Ibadan da kuma Fatakwal tsakanin watan Yunin 2018 da Disamban 2019.
  9. Daga Fatakwal, an sauya masa wurin aiki zuwa Abuja a matsayin Shugaban Kwalejin Bunkasa Kwarewa ta the EFCC da ke Karu.
  10. Ya samu horo daga hukumar FBI ta kasar Amurka da KPMG ta Birtaniya da wasu cibiyoyi da hukumomin Birtaniya da Najeriya.