Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya ki sa hannu a kan kudirin dokar da ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa suka gabatar masa a wani bangare na yin garambawul ga Dokar Zabe ta 2021.
A wasikar da Shugaban ya rubuta wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, ya ce irin matsalolin da kasar take fuskanta ya sa ba zai sanya hannu a kan kudirin dokar ba.
- Za a hau jirgin kasa kyauta tsawon mako 1 albarkacin Kirsimati – Gwamnati
- Babangida na son Osinbajo ya yi takarar shugaban kasa
Daga cikin dalilan da ya bayyana a wasikar, Shugaba Buhari ya ce irin makudan kudin da zaben ’yar tinke na jam’iyyu zai ci da kalubalen tsaro da za a fuskanta wurin gudanar da shi, na daga cikin dalilan da ya duba da suka hana shi sa wa kudirin hannu.
Haka ma ya yi batun hakkin da ’yan kasa suke da shi da kuma ware kananan jam’iyyu daga tafiyar.
Dama batun zaben fid-da- gwani ta hanyar ’yar tinke, shi ne babban abin da ya janyo takaddama a gyaran-fuskar da aka yi wa dokar zaben.
Tun farko wadansu daga cikin ’yan majalisar sun sha alwashin aiki da ikon da kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba su, na tabbatar da dokar ko da Shugaban Kasa bai sa mata hannu ba.
Sai dai a yanzu za a iya cewa lamarin ya sauya salo, kuma matakin na Shugaban Kasa ba lalle ya yi wa da dama daga cikin ’yan majalisar dadi ba.
To amma Shugaba Buhari ya nanata wa majalisar cewa ba ya yi gaban kansa ba ne wurin daukar wannan mataki.
A cikin wasikar ya fadi cewa ya nemi shawarwari daga ma’aikatun da suke da ruwa-da-tsaki a harkar, ya kuma yi nasa nazarin bisa la’akari da halin da kasar nan take ciki.
Ya ce hakan ya sa a karshe ya ga cewa abu mafi dacewa shi ne a kyale jam’iyyu su zabi yadda suke so su gudanar da zaben fid- da-gwanin da zai tsaya musu takara a kowane mukami.
Wadansu ’yan majalisar sun fara kumfar baki bayan da suka ji shiru daga Shugaba Kasa, yayin da wa’adin sanya wa kudirin dokar hannu ya wuce.
Hakan ya sa wadansu daga cikinsu shan alwashin aiki da ikon da Tsarin Mulki ya ba su, na tabbatar da dokar ko da Shugaban Kasa bai sa hannu ba.
Wadansu mutane suna zargin gwamnonin jihohi da kai -komo don ganin cewa Shugaba Buhari bai amince da garambawul din ba.
Masu sharhin siyasa na ganin cewa kin sa hannu da Shugaban ya yi wani mataki ne da zai yi wa gwamnonin dadi, domin ana zargin cewa da dama daga cikinsu ba sa goyon bayan zaben ’yar tinke wurin tsayar da ’yan takara a jihohinsu.
Su kuma ’yan majalisa suna ganin zaben ’yar tinken hanya ce da za ta kawo wa gwamnonin cikas kan babakeren da ake ganin suna yi wurin tsayar da ’yan takara.
Bayanai sun ce tuni sanatoci sun fara karbar sa hannu don tabbatar da dokar duk da Shugaban Kasa bai sanya mata hannu ba.