✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa kasuwarmu ta samu shugabanni 3 – Nura Babba

Alhaji Nura Babba wani dan kasuwa ne a Sabuwar Kasuwar Panteka da ke Kaduna. A wannan tattaunawar da Aminiya, ya yi bayanai a kan halin…

Alhaji Nura Babba wani dan kasuwa ne a Sabuwar Kasuwar Panteka da ke Kaduna. A wannan tattaunawar da Aminiya, ya yi bayanai a kan halin da kasuwar take ciki da dai sauransu. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Wane irin harkar kasuwanci kake yi a wannan kasuwa ta Sabuwar Panteka da ke Kaduna?
 Alhaji Nura: Da farko dai sunana Alhaji Nura, amma an fi sani da Nura Babba kuma nine Shugaban Bangaren Hausawa kuma daya daga cikin shugabannin kasuwan dungurungun. Kuma ina sana’ar saye da sayar da kayan mota wanda kuma na fi shahara ne a harkan injin moto wato wanda aka fi sani da suna ’yan Kotono.
Aminiya: Ina kake zuwa domin sawo wannan injuna?
Alhaji Nura: Ina zuwa kasashe da nisa domin sayo injin mota don nemam na sawa a bakin salati. Ina dangana wa da kasar Malesiya don wanna harka. Idan na je kasuwannin Ladipo ko na Oyingbo da garin Ikko da ke Jikar Legas ban sami kayan da ne ke bukata ba. Abin da ya sa bana zuwa Japan shi ne yadda wani wanda ake cewa Oke Japan ya yi kaka-gida a kasuwan Japan don sawo kaya zuwa Najeriya, inda kusan idan ba shi ba, ba su cika sake wa kowa don yin kasuwanci ba. Shi dan kabilar Ibo ne mazaunin garin Ikko.
Aminiya: Shin wane irin kallo ake yi muku idan kun yi wannan tafiya mai nisa don sawo tsofaffin kaya ba sababbi ba?
Alhaji Nura: A dangane da harkan kasuwanci irin na saye da sayarwa, ana yi wa Najeriya dariya ne idan mun je kasuwannin kasashen duniya domin sawo injinan mota wadanda aka taBa yin amfani da su ko kuma wanda aka yi hadari da mota sai aka cire injin, sannan mu kuma mu sawo su mu yi fito mu kawo Najeriya. Lallai a kasar Malesiya ana cewa ‘me ya sa ’yan Najeriya ke zuwa takanas ta Kano domin sayen kayan mota tsofaffi maimakon sabbi duk da an ce kasar nan nada arzikin man fetur, amma sai na yi biris kaman ban ji ba. Don haka nake bukatar wannan gwamnati da ta inganta darajar Naira yadda kasuwanci zai zamo da dadi da riba.
Aminiya: Me ya sa kasuwar take da shugabanni har Bangarori uku na Hausawa da Yarbawa da na Ibo?
Alhaji Nura: Sanin darajar jama’a ya sa aka zaBe ni a matsayin daya daga cikin shugabannin ’yan kasuwa na Sabuwar Panteka, amma a Bangaren Hausawa. Dalilin da aka raba Bangarorin shi ne domin kowa ya fi jin dadi yin magana, ko kai kara ko mai da bahasi da harshensa ga wanda ya san harshensa da al’adunsa. Wannan ya sa ake da shugaban Hausa da Ibo da kuma na Yarbawa amma kuma a karkashin kungioya babba guda daya, inda ko wace bangare ke binsa sau da kafa.
Aminiya: Ya ya fasalin harkar kasuwar yake?
Alhaji Nura: Kasuwar tana da Bangarori da dama kamar na masu saye da sayar da injin da bodin mota da masu sayar da giyan mota da masu sayar da taya da masu sayar da gilashi da masu sayar da taya da dai sauransu.
Aminiya: Ko mene ne matsolin kasuwar?
Alhaji Nura: Abin daya ke ci mana tuwo a kwarya shi ne yadda gwamnati musammman ma ta karamar hukumar Kaduna ta Kudu ta kasa gyara mana hanyar ruwa, yadda ko wane shekara ruwa ke yi mana ambaliya da yi mana Barna ga dukiyoyinmu duk da muna biyan kudin haraji wato kudin shiga ga karamar hukumar Kaduna ta Kudu, amma an dade ana yi mana gafara-sa har yanzu ba mu ga kaho ba.
Aminiya: Me ye kiran ka ga gwamnati?
Alhaji Nura: Muna kira ga wannan gwamnati da ta yi wa harkar kasuwanci garanbawul don kudin shiga da ake biya ayi amfani da shi don inganta kasa baki daya.Da kuma inganta wannan kasuwa ta hanyar gyara hanyar shiga kasuwar da magudanan ruwa da tsaro don kasuwar ta shiga halin ha’ula’i.