✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa kasuwar hannun jari ke jan kafa

Ga alamu tsammanin da masu zuba jari suka yi na ganin kamun ludayin sabuwar gwamnati shi ne ya janyo hannun jarin kasuwar yake yin tafiyar…

Ga alamu tsammanin da masu zuba jari suka yi na ganin kamun ludayin sabuwar gwamnati shi ne ya janyo hannun jarin kasuwar yake yin tafiyar hawainiya.

kwararru sun bayyana cewa masu zuba jari suna dari-dari saboda haka sun zaku su ga inda sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta sa gaba.
Hakan shi zai ba su damar sayen hannun jarin da suke so daga kamfanonin mabambanta don samun riba mai yawa.
Wannana shi ya janyo hannun jarin kasuwar yake kwan-gaba, kwan-baya a cikin makon da muke ciki.
A ranar Talatar da ta gabata hanun jarin kasuwar ya dan samu tagomashi da kashi 0.05 ko kuma maki 17. 24 daga maki 34, 044.65 zuwa maki 34,061.89.
Hakazalika, kasuwar ta karu da biliyan shida daga naira tiriliyan 11 da biliyan 568 zuwa naira tiriliyan 11 da biliyan 574.
An yi hadahadar hannun jarin jumillar miliyan 224 da dubu 72 wanda ya kai naira biliyan uku da miliyan 478 a hadahada dubu uku da 940, inda hanun jarin kamfanoni 26 suka samu riba, kamfanoni 19 suka yi asara.
Kamfanin bONO ya samu riba a ranar Talata, inda hannun jarinsa ya tashi da kashi 9.60 ko kuma kwabo 17 ya rufe kasuwar da a naira 1.94 a kowane hannun jari.
Kamfanin Ginegine na Costain da kamfanin dangote Flour Mills and Libesstocks Feeds da kamfanin sarrafa wayoyin lantarki na Cutid sun samu riba.
Amma kamfanin Inshora na International Energy Insurance Plc da kamfanin dab’i na Academy Press Plc da kamfanin bankin kananan ’yan kasuwa na NPF Microfinance bank Plc hannun jarinsu ya yi kasa.
A ranar Litinin din da ta gabata bayan an rantsar da sabuwar gwamnati, hanun jarin kasuwar ya fadi da naira biliyan 90 ko kuma kashi 0.77 daga naira tiriliyan 11 da digo 658 zuwa naira tiriliyan 11 da biliyan 568.