✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa kamfanin Twitter zai rage ma’aikata 336

Kamfanin Twitter ya ce zai rage guraben ayyuka 336, na ma’aikatansa a wani bangare na sake yin gyare- gyare ga harkokin kasuwancinsa, kamar yadda kafar…

Kamfanin Twitter ya ce zai rage guraben ayyuka 336, na ma’aikatansa a wani bangare na sake yin gyare- gyare ga harkokin kasuwancinsa, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.

Rage guraben ayyukan zai ci tsakanin Dala miliyan 10 da Dala miliyan 20 na kudin sallama.
Yayinda gyare- gyaren zai ci tsakanin Dala miliyan 5 da kuma Dala miliyan 15 inji kamfanin Twitter.
Hannayen jari a Twitter sun tashi da kashi 2% bayan sanarwar da aka yi a makon jiya.
Wannan mataki na zuwa ne wasu ‘yan kwanaki bayan da aka tabbatarwa da Jack Dorsey kujerar babban jami’in gudanarwa na dindindin a kamfanin.
Mista Jack ya rike mukamin shugaban kamfanin na rikon kwarya har tsawon watanni uku bayan da Dick Costolo ya sauka a ranar 1 ga watan Yulin bana.
A wata wasika da ya aike wa ma’aikatan Twitter, Mista Dorsey ya rubuta cewa: “Mun dauki shawara mai wahalar gaske muna shirin sallamar mutane 336 daga kamfanin nan.””
Wadanda za a sallama dai sun kai kaso kashi 8 cikin 100 na yawan ma’aikatan kamfanin, wanda yake ikirarin yana da ma’aikatan da suka kai 4100.
Wasu mutane hudu ne dai suka kafa kamfanin a Jihar Kalifoniya ta kasar Amurka a shekarar 2006.