✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa aikin gyaran hanya tafiyar hawainiya

Najeriya na bukatar Naira tiriliyan 6.26 domin kammala ayyukan manyan hanyoyi 711.

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ya ce ma’aikatarsa na bukatar Naira tiriliyan 6.26 domin kammala ayyukan manyan hanyoyi 711 a fadin Najeriya.

Da yake kare kasafin ma’aikatarsa na 2021 da yadda ta sarrafa na 2020, Fashola ya ce rashin ba da isassun kudade ne ke sa ayyukan manyan hanyoyin tafiyar hawainiya.

“Yanzu haka ma’aikatarmu na aiwatar da ayyukan 711 na gina manyan hanyoyi kuma zuwa ranar 1 ga Oktoba 2020, bashin da ‘yan kwangila ke bin ta kai biliyan N392.020”, inji shi.

Ya shaida wa Kwamitin Ayyukan na Majalisar Tarayya cewa daga cikin Naira biliyan 227.96 na mayan ayyuka da aka ware wa ma’aikatarsa a kasafin 2020, an ba ta Naira biliyan 152.150 wadanda aka yi amfani da su a bangarn ayyukan da samar da gidaje.

A cewarsa adadin kudaden da aka karba shi ne kashi 66.74 na kasafin ma’aikatar, yayin da har yanzu ba a saki ragowar Naira biliyan 75.818 ba.

Ya ce Naira biliyan 162.559 daga cikin kudin kasafin ma’aikatar na 2020 an samar da su ne daga tsarin takardun rance na Sukuk.