✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya farfaɗo da ’yan Chamama a Kannywood — Sani Dan Gwari

Sani Dan Gwari ya jima yana sa mutane nishaɗi ta yadda yake kwaikwayar Hausar gwarawa. Wasu na ganin cewa Dan Gwari, Gwarin ne a zahiri,…

Sani Dan Gwari ya jima yana sa mutane nishaɗi ta yadda yake kwaikwayar Hausar gwarawa.

Wasu na ganin cewa Dan Gwari, Gwarin ne a zahiri, amma a cikin wannan tattaunawa da ya yi da Aminiya ya fayyace ko wa ye shi da burinsa da kuma wasu batutuwa.

Ko za ga gaya mana ɗan taƙaitaccen tarihinka?

Sunana Sani Ibrahim. Ni mutumin garin Tsiga ne a Ƙaramar Hukumar Bakorin Jahar Katsina. Amma a Jihar Kaduna aka haife ni ranar 5 ga watan Mayun 1975. A nan na yi karatun firamare da na sakandare, duk da cewar ban samu na gama makarantar sakandaren ba, sakamakon rasuwar iyayena.

Daga nan fafutukar nemar wa kai makoma a rayuwa ta sa na fara koyan aikin walda. Ina cikin koyan aikin waldar ce na shiga ƙungiyar wasan kwaikwayo na daɓe. Na kasance mamba na ƙungiyoyin wasan kwaikwayo da dama, wanda hakan ya kai ni ga kasancewa cikin fittaccen dandalin wasannin gargajiyan nan wato ‘Gidan Kashe Ahu’ da kuma wasu wassannin da ake yi a gidajen radiyo. Yanzu haka dai, ni dan wasan kwaikwayo ne mai shirya fim kuma mai sana’ar walda.

Yaya aka yi ka tsinci kanka a da’irar shirya finafinan Kannywood?

Na shigo Kannywood ne sakamakon alaƙata da shahararren mai wasan barkwancin nan, marigayi Rabilu Musa Ibro. Na hadu da shi ne a lokacin muna ganiyar wasanninmu na daɓe kuma bisa al’ada mukan gayyato wasu fitattun ’yan wasan kwaikwayo zuwa inda muke wasanninmu. A irin haka ne muka gayyato shi marigayi Ibro. Bayan ya zo, an kuma yi wasa an gama sai ya nuna buƙatar in dawo wurinsa nan Wudil da ke Kano.

Ban yi ƙasa a gwiwa ba, na amshi wannan gayyata da ya yi min. Ta haka na dawo Kano wurin marigayi Ibro. Da dawowata wurinsa na tsunduma cikin da’irar Kannywood, Allah cikin ikonSa ba da dadewa ba, fuskata ta zama fitacciya ta cikin fim din ‘Ibro Dan Ruwa’. Cikin dan ƙanƙanin lokaci na zama fittace a cikin finafinan Ibro da ake wa laƙabi da ‘Chamama’. Ina nan wurin marigayi Ibro har Allah Ya karɓi ransa.

Marigayi Ibro ya taimaka wa rayuwarmu a wannan harkar, saboda haka ba za mu taɓa mantawa da irin gudunmuwar da ya bai wa wannan harkar ba da kuma irin wacce ya ba mu a matakin daidaiku da kuma matakin ƙungiya.

Shin yaya aka yi ka yi fice wajen kwaikwayon Hausar Gwarawa kuma kai ba Gwari ba?

Gaskiya abin ya samo asali ne daga yawaita mu’amula ta da mutanen Gbagy, wadanda aka fi sani da Gwarawa.

Da farko dai makarantar firamaren da na yi a Kaduna, tana cikin unguwar Gwarawa kuma ina yawan mu’amala da su sosai. Ta hakan, na fuskanci yanayinsu da kuma sauran al’amura da suka shafi rayuwarsu. Hakazalika, na zauna a garuruwan Gwarawa da ke Abuja da Jihar Neja da ma wasu wuraren.

Kasancewata cikinsu da kuma yadda na fusknci cewa kwaikwayonsu ya zame mani hanyar neman abinci, su suka sa na zage dantse wajen ganin na ƙware wajen kwaiwayon yadda Hausarsu take da kuma yadda al’adadunsu suke.

Bayan shafe kimanin shekaru fiye da ashirin a Kannywood, yaya za ka kwatanta ci-gaban da aka samu?

A gaskiya zan iya cewa masana’antar Kannywood ta samu gagarumin ci-gaba ta fannin kayan aiki da kuma yadda ake gudanar da sana’ar.

A inda kawai nake ganin kamar akwai sauran gyara shi ne ta yadda a yanzu aka fi karkata wajen bai wa daidaikun jarumai mahimmanci, maimakon gina labarai masu jigon da ba su buƙatar a ce sai an sami wata sananniyar fuska kafin labarin ya motsa.

Hakan ya haifar da tsaiko a masana’antar ta yadda sababbin fuskoki suke samun tasgaro da sassarfar samun dammar kaiwa gaci a ƙanƙanin lokaci.

Duk da haka, ni ina ganin masana’antar za ta kai gaɓar da duniya za ta yi alfahari da ita, domin a halin yanzu harkar tana ta samun karɓuwa da daukaka.

Me za ka iya cewa game da sana’ar fim?

Sai hamdala, sana’ar fim ta yi min komai, domin Allah cikin ikonSa Ya sa na samu duk wani abu da na samu ta hanyar fim. Na yi gida, na yi mota na kuma yi aure duk ta dalilin fim. Hakazalika, na kewaya garuruwa da dama har ma da wasu ƙasashen duk ta dalilin fim. Ya zama wajibi in gode wa Allah.

A gaskiya, ba domin fim ba, da ba na jin zan kai inda nake a yau. Na hadu da manyan mutane, na hadu da manyan attajirai da manyan ma’aikata. A wannan sabgar, an ba ni kyautar gida, an ba ni kyautar mota, har kyautar mace an ba ni.

Me za ka yi da a ce ba ka harkar fim?

Walda mana. Kar ka manta na shaida maka tun da fari cewa, bayan na bar karatu na koma koyan walda ce. Saboda haka, ban bar wannan sana’ar ba. Ko yanzu haka ina da garejin walda a garin Kaduna. Don haka, in ba na wajen yin fim, to kuwa ina wajen aikin waldata saboda na koya, na kuma iya.

Ana raɗe-raɗin ka koma garin Jos bayan yawan ganin ka da Ɗan Angas da ake yi. Mece ce gaskiyar wannan maganar?

Ba komawa Jos na yi ba, amma ka san yanayin aiki irin namu babu inda ba za a gan ka ba. Ɗan Angas dai mutum ne mai barkwanci, wanda yana da tasa kafar da yake yada irin tasa fasahar. Cikin ikon Allah, sai ya ga ya dace ya nemo ni, mu riƙa yi tare. A gaskiya Ɗan Angas ya tallafa wa harkar domin yakan gayyace ni Jos, in yi kwanaki muna neman abinci.

Dole in gode masa bisa amanna da nagartata da ya yi wajen zaɓo ni cikin mutane da yawa da ke wannan da’irar.

Yaya za ka kwatanta rayuwa bayan mutuwar mai gidanka Ibro?

Bayan rasuwar Ibro, ni kaina na za ci na ƙare harkar fim. Ba ma ni kaina ba, duk wani dan tawagar Ibro sai da ya tsinci kansa a irin wannan yanayi. Allah cikin ikonSa da yake an dan san ni a harkar, hakan ta sa na ringa samun ayyukan fim kadan­kadan. Daga baya na fara shirya fim da kaina don dai dan-adam ya samu, ya motsa.

Ana haka Allah Ya kawo fim din barkwancin na ‘Gidan Badamasi’ wanda shahararren mai ba da umarni Falalu Dorayi ya shirya. Gaskiya Gidan Badamasi ya taimaka matuƙa wajen farfado da ’yan wasa da dama. Domin shi ya yayyafa mana ruwa, muka farfado. Zan iya cewa, ba don wannan shirin ba, da wasu daga cikinmu an dade da mance kamanninsu a harkar Hausa fim.

Mene ne burinka a wannan harkar?

Burina shi ne, in ga na farfado da yanayin wasan barkwanci irin wanda uban gidanmu marigayi Ibro ya assasa. Zan so a ce na dawo da ragowar ’yan wasan da suka rage don mu ci gaba daga inda marigayi Ibro ya tsaya.

Shin Ɗan Gwari na da aure?

Ƙwarai kuwa, ina da aure. Matana biyu, amma Allah Ya yi wa daya rasuwa kuma ina da ’ya’ya 11.