✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ke kawo cikas ga hakar man fetur a Arewa

Sakamakon yadda ake ta cewa an gano wuraren da ke da arzikin man fetur a Arewa inda a baya-bayan nan Jihar Filato ta shiga sahu,…

Sakamakon yadda ake ta cewa an gano wuraren da ke da arzikin man fetur a Arewa inda a baya-bayan nan Jihar Filato ta shiga sahu, ba tare da kammala ko daya a tsawon tarihin ayyukan ba, Aminiya ta zanta da wani kwararren injiniya a bangaren, Injiniya Yabagi Yusuf Sani, wanda tsohon babban jami’i ne a Kamfanin NNPC.

Ya bayyana dalilan da ke jawo matsalar kuma ya ba da shawarar yadda za a kai ga nasara:

Wadanne yankuna ne a Arewa aka ga gano man fetur zuwa yanzu?

Akwai wurare biyar da aka tabbatar da suna da arzikin man fetur da gas: sun hada da Tafkin Chadi a Jihar Borno da Sakkwato da Tafkin Bidda, da wani yanki da ake takaddama tsakanin jihohin Kogi da Anambra.

Ga na iyakar jihohin Bauchi da Gombe da kuma yankin Benuwai, sai kuma na baya-bayan nan da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya sanar an gano a yankin Wase da ke Jihar Filato.

Sai dai hasashe ya nuna cewa kusan kowace jiha a Arewa tana da man fetur da gas, ban da jihohi biyu wato Kano da Katsina.

Tushen mai da ke wadancan wurare da na lissafo a baya ne suka gewaya zuwa sauran jihohin.

A kimiyyance wurare ne da ’yan Adam da dabbobi suka taba rayuwa shekaru aru-aru, kasusuwansu da itatuwa suka narke sannan suka samar da sinadaran man.

Akwai kuma bincike da ya nuna cewa a baya, teku ya taba kaiwa ga wadancan wurarare da ake kira da tafki (basin a Turance), kafin ya ja baya, ya koma inda yake a yanzu.

To a wadannan wurararen ne ake samun man fetur da iskar gas. Ingancin man Arewa ya nuna, ya dara wanda a ke da shi a Kudu, kamar yadda binciken ya nuna a baya.

 

Ko adadinsa ya kai matakin kasuwanci?

Zan ba ka misali da wuri guda inda na kasance daya daga cikin ’yan kwamitin da Jihar Neja ta kafa a lokacin Gwamna Mu’azu Babangida Aliyu.

Daga gwaje-gwajen da aka yi akwai wanda muka kai kasar Jamus ta hanyar kai wasu ma’adinai da muka gano a wuraren, binciken ya tabbatar da cewa adadi ne mai yawa.

Sai dai matsalar da aka samu a lokacin ita ce, an sa siyasa a lamarin. Ko da muka samu damar ganin jagororin Kamfanin NNPC na wancan lokaci, ba mu samu cikakken hadin kai da ake bukata ba.

Mun rubuta wa gwamnati takarda a wancan lokaci muka nuna irin siyasar da aka yi a kai a baya. Duk wuraren da ke da arzikin mai a tafkuna, biyar a Arewa suke, uku ne suke Kudu.

 

Yanzu me kake gani ya jawo jinkirin aikin?

Dole a yaba wa gwamnatin Shugaba Buhari kan nuna sha’awar yin aikin da kuma dagewa da ake yi a kai. Sai dai koda gwamnatin ta zo farashin mai ya ci gaba da karyewa a kasuwar duniya.

Sannan aikin hakar mai, lamari ne da ke bukatar dimbin kudi. Shi ya sa duk inda ake yin aikin na hadin gwiwa ne a tsakanin gwamnatoci da kamfanoni.

Matsalarda aka samu a nan ita ce kamfanonin mai da ke gudanar da harka a kasar nan, sun fi sha’awar gudanar da aikin a yankin Neja-Delta, da suka fi tabbaci a kai kuma suke da saukin daukarsa zuwa teku, zuwa inda za su kai ga kowace kasuwar duniya a cikin sauki.

Haka sun fi samun sauki wajen kawo kayan aikin hakar man da kuma abin da injunansu ke bukata na yau da kullum.

Har ila yau wuraren da ake maganar mai a Arewa ba waje daya da aka kai ga karasa aikin.

Abin da ya kamata gwamnati ta yi a nan shi ne, ta kirkiro sababbin dokoki a harkar mai da za su tilasta wa duk wani kamfanin da yake aikin mai a gabar ruwa, ya yi na kan tudu ko da guda daya ne a wannan yanki.

In ba haka aka yi ba yana da wuya gwamnati kadai ta iya gudanar da aikin a kan lokaci. Saboda gwamnatin na bukatar kudi wajen aiwatar da sauran bangarorin gudanar da kasa.

Akwai wata hanyar ta daban, wadda ita kuma a matakin gwamnatocin jihohin yankin ne. Kowane Gwmana a Arewa ya rika ware kashi 2 cikin 100 na kasafin kudin shekara ga aikin.

Wannan zai ba wa kowace jiha dama ta ci gajiyar bangaren hannun jari a aikin idan ya kare tare da Gwamnatin Tarayya.

Ba na mancewa da wani kwamiti a baya da na kasance a ciki kan lamarin, mun gana da kwamishinonin kudi na jihohin Arewa inda muka gabatar musu da wannan shawara.

Tattaunawa ta yi nisa, sai dai ba a jima ba sai ga zaben shekarar 2015, shi ke nan sai aka mance da batun.

Yanzu aikin hakar mai ya kara sauki, an samu na’urori masu karfi da saurin gudanar da aiki. A cikin shekara hudu zuwa biyar ana iya yin komai.

 

Kamar wadanne abubuwa ake samu a arzikin mai baya ga kudi?

Zai bunkasa dukkan bangarorin tattalin arziki.

Na farko a bangaren gas zai samar da tsayayyiyar wutar lantarki da masana’antunmu ke matukar bukata.

Ga bangaren sinadarai da masana’antu ke bukata ciki har da na sutura da na taki da roba da kuma nau’o’in man mota da na shafawa, ga kuma sinadarai da dama.

Duk da dai lokaci na kurewa sakamakon ci gaba da ake samu wajen kirkiro abubuwa da ba sa bukatar mai kamar mota da kuma koma wa bangaren wasu nau’o’in mai da ake samar da su daga sinadaran da aka fi sani da green (man fetur daga itatuwa) ko renewable energy (amfani da hasken rana da makamantansu).

Amma duk da haka bangaren gas zai ci gaba da tasiri kuma sinadaran da shi kansa man fetur ke samarwa, za a ci gaba da bukatarsu a masana’antu.