Gwamnatin Jihar Kano, ta fara rabon kayan makaranta kyauta ga ɗalibai 789,000 a makarantu 7,092 na gwamnati da ke faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf ne, ya ƙaddamar da shirin a wani biki da aka gudanar a Fadar Gwamnatin jihar a ranar Litinin.
- Har yanzu Aminu Ado Bayero ne Sarkin Kano – Tsohon Kwamishinan Shari’a
- An tsige Shugaban Majalisar Dokokin Legas
Ya bayyana cewa wannan shiri zai tabbatar da cewa dukkanin yara sun samu ingantaccen ilimi tare da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
“A yau, muna rabon kayan makaranta 789,363 masu inganci ga ɗalibai a makarantun gwamnati.
“Kowanne yaro zai samu riguna biyu kyauta. Wannan zai rage wa iyaye nauyin kuɗi da kuma ƙarfafi yaranmu su riƙa zuwa makaranta,” in ji Gwamna Abba.
Gwamnan ya jaddada cewa kayan makarantar za su ƙara wa ɗalibai ƙwarin gwiwa tare da samar da ingantacciyar muhalli don koyarwa.
Ya umarci shugabannin ƙananan hukumomi, ƙungiyoyi, kwamitocin makarantun, malamai, sarakunan gargajiya da malaman addini su tabbatar da cewa kayan makarantar sun isa hannun kowa cikin gaskiya da adalci.
Gwamna Abba, ya kuma sanar da haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da Bankin Bunƙasa Musulunci (IsDB), don gina makarantu huɗu na koyarwa da harshen Turanci da Larabci.
Bugu da ƙari, ya ce an farfaɗo da shirin makarantu na Tsangaya, inda za a kammala ginin wasu makarantu domin bai wa almajirai damar samun ilimin zamani tare da rage yawan yara a kan tituna.