✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A yi hakuri: Komai nisan jifa kasa za ta fado

Ranar Asabar din karshen makon da ya gabata ne shugaban Hukumar Zabe mai zaman kanta, wato INEC, Farfesa Attahiru Jega ya fada wa taron manema…

Ranar Asabar din karshen makon da ya gabata ne shugaban Hukumar Zabe mai zaman kanta, wato INEC, Farfesa Attahiru Jega ya fada wa taron manema labarai bayan wani dogon taro da Hukumar ta yi da shugabannin jam`iyyun siyasa da na kungiyoyin kare hakkain bil Adama da Kwamishinonin Hukumarsa na kasa da na jihohi cewa bayan waccan doguwar tattaunawa, Hukumar ta yanke shawarar dage zabubbukan kasa da ta shirya gudanarwa tsakanin ranakun 14 da 28 ga wannan watan na Fabrairu, har zuwa ranar 28 ga watan Maris da kuma 11 ga watan Afrilu masu zuwa.  Dama dai an dade musamman tsakankani shugabannin manyan jam`iyyun kasar nan biyu, wato PDP mai mulki da gwamnati tsakiya da kuma jam`iyyar APC, babbar jam`iyyar adawa da kungiyoyin kare hakkin bil Adama na ciki da wajen kasar nan kai har ma da manyan kasashen duniya irin su Amurka da Birtaniya ana ta cece-ku ce akan akan cancanta da rashin cancanta rdage zabubbukan. An dade ana rade-radin shugaba kasa Dokta Goodluck Jonathan da jam`iyyarsa ta PDP, suna aiki tukuru a karshin kasa don neman a dage zabubbuka. Har sai ranar 22 ga watan Janairun da ya gabata lokacin da mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki (mai ritaya) a wani jawabi da ya yi a Chartham House da ke birnin London ya shawarci Hukumar ta INEC da ta dage gudanar da zabubbukan.
Babban hamzarin da Kanar Dasuki ya bayar a Landan din wai shi ne akwai jinkiri wajen rabon katin kada kuri`a na din-din-din, da Hukumar ta INEC ta ke yi. Amma mai karatu, kar ka manta kwana daya kafin ya bayar da waccan shawara a London, mai ba shugaban kasar shawara akan harkokin tsaro, anan gida ya yi wani bayani akan matakan tsaro ga jami`an Hukumar ta INEC gaban manyan Hafsoshin dakarun tsaron kasa, inda ya shawarci Hukumar ta INEC, akan bukatar da ke akwai na ta dage gudanar da zabubbukan saboda wai jami`an tsaron sun sanar da shi suna gaf da fara wani gagarumin aikin kai farmaki ga `yan kungiyar Ahlis Sunnah Lid-Da`awati Wal-Jihad da ake ma lakabi da Boko Haram a shiyyar Arewa maso Gabas da aniyar ganin kawo karshe hare-haren da suke kaiwa a shiyyar, musamman a jihohin Barno da Yobe da Adamawa da sauran jihohi.
Waccan shawara da kiran da Kanar Sambo, ya yi a daidai lokacin da ake cewa ya rage kasa da wata daya a fara zabubbukan, ba ko shakka ya jefa mutanen kasa cikin kogintunanin anya kuwa gwamnatin tarayyar za ta gudanar da zaben a bana kamar yadda kundin tsarin mulki da na zaben suka tanada. Ba don kome ba kuwa, sai don irin yadda gwamnatin tarayyar ta yi biris da hare-haren `yan Boko Haram duk tsawon lokacin na sama da shekaru biyar suna gwagwarmayarsu a cikin kasar nanhar sun kama wasu kananan Hukumomi da suka kira Daularsu ba tare da gwamnatin PDP ta tarayya ta dauki wasu kwararar matakan kawo karshen al`amarin.
Bayan jin wannan kira na mai bada shawarar akan harkokin tsaro ga shugaban kasa, sai kuma ga shugabannin wasu jam`iyyun siyasa 16, da wasu `yan takarar neman shugabancin kasa a babban zaben da aka dage su 5, sun  fara kiraye-kirayen lallai sai`Hukumar ta INEC ta dage zabubbukan na 14 da 28 ga wannan watan. Babban hanzarin da Kakakinsu kuma dan takarar neman shugabancin kasa a inuwar jam`iyyar UDP, Cif Godson Okoye, ya shi ne irin wanda Kanar Dasuki ya fara bayarwa na gaza samar da katuttukan din-din-din na kada kuri`a, wanda suka kira tamfar tauye hakkin“yan kasa ne da kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar masu.
Kamar kiraye-kirayen a daga zabubbuka za su tsaya a haka. Can kuma sai ga wata zanga-zangar lumana da wasu `yan tsirarun matasa da ake zargin sojoji haya ne da jam`iyyar PDP ta hayo daga kauyukan da suke kewaye da Abuja, wadanda suka gudanar da zanga-zanga har karo biyu zuwa Hedkwatar Hukumar ta INEC a Abuja da korafe-korafen lalle sai a dage zabubbukan, suma hanzarinsu shi ne na rashin kamala raba katuttun kada kuri`a. A gefe daya suma jam`iiyyun adawa sun samu nasu mutanen da suka gudanar da akasin waccan zanga-zanga, inda su kuma sukai kiraye-kirayen sai Hukumar ta INEC, ta ci gaba ta gudanar da zabubbukan kamar yadda ta tsara.
A lokacin da Ofishin shugaban kasa da ita kanta jam`iyyar PDP, suka fahinci ba makawa, Hukumar ta INEC, za ta gudanar da zabubbukan kamar yadda ta tsara, kwatsam da rana tsaka, sai shugaban kasa ya kira taron membobin Majalisar kasa, da ta kunshi tsofaffin shugabannin kasa da tsofaffin Cif Joji Jojin kasa  da mai ci yanzu da shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai da gwamnonin jihohi, sannan ya gayyaci shugabannin Hukumar ta INEC da manyan Hafsoshin dakarun kasar nan.
A taron Majalisar kasar da aka kwashe sama da awoyi bakwai ana tattaunawa, bayan an ji ta bakin Hukumar ta INEC, wadda ta sake nanatawa taron matsayinta na ita fa a shirye take ta gudanarda zaben a wadancan ranaiku. Amma sai ga shi duk da wancan tabbacin Hukumar, an dai ci gaba da samun sabanin ra`ayi akan gudanar da zabubbukan. Ya yin dagwamnonin jam`iyyar adawa ta APC suka goyi bayan a ci gaba a yi zaben, shi kuwa shugaban kasa da gwamnoninsu na jam`iyyar PDP tsayawa sukai akan sai a daga shi. Wannan kiki-kaka ta sanya Majalisar kasar wadda dama aikinta ta bada shawara, ta shawarci Hukumar ta INEC, akan ta koma ta sake yin tuntuba da dukkan masu ruwa da tsaki akan zaben kafin ta yanke hukunci.
Sakamakon taron tuntubar da Hukumar ta INEC ta yi da shugabannin jam`iyyun siyasa da na kungiyoyin kare hakkin bil adama da dukkan Kwamishinoninta na kasa da jihohi a ranar asabat da ta gabata, ya sa bayan taron Hukumar ta INEC, ta bada shelar cewa ta dage zabubbukan da makonni shidda kamar yadda jami`an tsaron suka nema, amma ba wai don ita bata shirya ba. An ji shugaban Hukumar ta INEC, Farfesa Attahiru Jega yana cewa “Tunda sojojin sun ce a daidai lokacin da ya shirya gudanar da zabubbukan ba za a samu sojojin da zasu bada kariyar tsaro ba ga ma`aikata da kayayyakin zabe da su kansu masu kada kuri`a, to kuwa ba su da zabin da ya wuce su dage zabubbukan zuwa wa`adin da jami`an tsaron suka nema na makonni shidda masu zuwa”.
Mai karatu, ka dan ji wani abu akan yadda ta kasance har aka ce a dage zabubbuka. Ba wani abu ya kawo wannan danbarwa ba kamar ydda wasu masu son a gudanar da zabubbukan suka yi zargi, illa gwamnatin PDP da shugaba Jonatahan sun gama lissafinsu kaf, sun kuma hango cewa ba makawa, muddin aka kada kuri`a sunan gwamnatinsa marigayi. Yanzu din ma da suka  bankara da karfin ikon da suke da shi, irin wadancan mutane na ganin da yardar Allah ba canja zane za ta yi ba. Inda suka ce aitusa bata hura wuta kuma kome nisan jifa dai kasa za ta fado. Abin fata anan, shi ne Allah Ya sa kafin ma cikar wa`adin makonni shidda Allah kawo mana karshen annobar da aka fake da ita aka dage zabubbukan. Ga `yan kasa a ci gaba da addu`a da hakuri. Komai nisan jifa dai kasa za ta fado.