Edita, yau sama da kwanaki 135, Ke nan da Satan Mata Yan Makarantan Chibok har Yau har gobe Babu su babu dalilin su Gwamnati Nigeria Sai karya da Yaudaran iyayen su ana ci gaba da kashe mutanen Arewa Maso Gabas da kona gidajen su, duk da haka ba a daukar matakin komai akan wannan kashe mutane. A gaskiya kiran iyayen matan chibok zuwa Abuja da Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya yi ba karamin cin mutunci ba ne, da ma wulakantasu.
Ya kamata shi Shugaba Jonathan ne yakamata ya je chibok yakai musu ziyarar Jaje da ma ta’aziyar kashe jama’ar da ake yi kanda Yanzu takai ga yau Karaman hukuman Danboa, dake Jjihar Borno bata hannun gwamnatin Najeriya Wakilan al’umma a Majlisar asa, ku dauki matakin korar manyan jami’an tsaro, sannan a nada wadanda suka shirya tunkarar kalubalen da ke fuskantar kasar nan. Daga Ahmadu Manager Daga Bauchi Unguwan Karofin Madaki a Najeriya.08065189242.
Addu’a ga Ebola
Allah Ya raba mu da cutar Ebola. Amin Daga Safiyya Ibrahim Magayaki, kwarbai Zariya 08165613936.
Mu yi juriya
Assalamu alaikum. Edita. Zuwa ga ’yan uwana Musulmi. A kowane lokaci mu kasance masu juriya da hakuri. Daga Sadiya Yaro Ali. 07059777325.
Shugaban Kwankwasiyya zalla
Aminiya don Allah ina son ku taya ni cigiyar Shugaban Kwankwasiyya Zalla, M. Muhammad Zakiru. Daga Isma’il alkyabba Funtuwa. 08063194418.
Mu dage da addu’a
Inna lillahi wa inna ilaihir Raji’un. Editan Aminiya wai mun ji an ce ’yan Boko Haram sun kori sojojin Najeriya har sun tsere zuwa Kamaru? Ka ga wannan ya nuna rashin adalcin Gwamnatin Najeriya karara. Don haka ina kira ga ’yan Arewa mu tashi tsaye mu yi ta yin addu’a. Idan tsanani ya yi yawa, sauki na zua daga Allah. Daga Hajiya Fatima ’Yar mutan Lajawa da Muhammad dan Chiranci, Dei-dei Abuja 07056991838.
Ga dan majalisar Maiyama Koko
Aminiya ki isarmin da sakoma ga dan majalisarmu mai wakiltar Maiyama Koko, cewa ba mu ga aikin da ya yi mana a Maiyama ba, sai dai wasu matasa 10 da ya samar wa aiki. To idan har bai kara kwazo wajen aiwatar da ayyukan alheri ba, ni ina ganin gara a shekara ta 2015 mu zabi wanda zai yi mana kyakkyawan wakilci da ayyukan raya kasa managarta. Tunda kun ga wannan ko ya yi wa talakawa aike, sai ya bari abin ya makale a wani wuri. Allah dai ya ba mu shugabannni nagari. Amin. Daga Nasiru Musa Maiyama Jihar Kebbi 08062206733/08084151555.
Ga gwamnan Kebbi
Aminiya ki mika godiyata ga Gwmanan Jihar Kebbi, a mamadadin ilahirin jama’ar Beere, saboda ayyukan raya kasa yake yi wa al’umma. Ina kuma rokon Mai girma Gwamna Alhaji Usman Nasamu dakin gari da ya tuna da wutar lantarki ta garin Beere a gundumar Alwasa a Argungu, tunda babban gari ne, kuma yana kusa da titi. Muna bukatar wutar lantarki. Daga Abdullahi danmama Beere 08038729955.
Ga sojojin Najeriya
Edita don Allah ka ba ni dama in nuna tausayawata ga sojojin wannan kasa. A gaskiya Allah Ya jarrabe mu da wasu shugabanni da har masu tsaronsu ba su tsira ba.. Allah Ya saukake. Daga Atiku Umar Katsina 08058408868.
Ga ’yan Najeriya
Jama’ar Najeriya mu kara hakuri, mu dage mu zabi jam’iyyar adawa ta APC, tunda mun ga irin kamun ludayin PDP. Irin mulkin nasu ya isa haka nan. Muna neman canji. Allah Ya taimake mu. Daga Sani Abdu Beta 07068223015.
Ga iyayen ’yan mata
Assalamu alaikum. Edita don Allah ka ba ni dama in yi kira ga iyayen yara, ya kamata a rika saukaka wa domin su samu damar yin aure. Saboda wallahi mafi yawa masu karamin karfi ne, amma da zarar iyayen sun fahimci ba shi da komai sai a hanaka, koda halayenka nagari ne. Daga Jameel Gambo Takai, Kano 08094571634.
Rayuwar ’yan Najeriya
Rayuwar al ummar Najeriya musamman talakka, inda ya ki karatu, ya ki aiki yayi wahalar samu, kuma idan ya tashi yin wata sana’a, abin da ban tausayi ga , domin yau sai dai Allah shi ne gatan wanda bai da wadata da kuma mai yi domin sa, amma idan rashin lafiya ta samu maras shi hatta gaishe shi abune ai wahala, Allah ya kawo mana daukin shugabanci na adalci. Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina, 07066434519.
Godiya ga amtasan Sakkwato
Salam Edita ga godiyarmu ga’ya’yan kungiyar Matasa ta Youths Coalition Of Sokoto State a bisa Zanga-Zangar Lumana da suka gabatar a Ranar Laraba da ta gabata. Domin nuna rashin amincewarsu da yunkurin Gwamnatin Jihar Sakkwato na ciwo bashin Bilyan uku, da Milyan 600, wanda wannan bashin babu inda za a karkata shi illa ga batun Kamfe da sauran almubazzaranci da kudin alhali dimbin matasa ke ta gararamba a kan tituna tamkar ledojin Pure-Water. Daga Hassan Muhammad Binanchi,Daga Unguwar Magajin Garin Sokoto a Tarayyar Najeriya 08022046393.
Ga Aminiya
Salam Edita ina yi muku fatan alkhairi Allah ya kara daukaka Jaridar Aminiya. Daga Salisu Bashir [email protected].
Ga Sarkin Daura
Edita akalla na kai wajen wata 14 ina turo sako, amma har yau ban g ako daya ba. To ka isar min da addu’ar fatan alkhairi ga Mai amrtaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk. Allah Ya kara masa imani, ya kare sarki daga sharrin abin hawa. Amin. Daga Sadi Tsohon Sarki Daura 08085127726.
Ga manyan kasata
Assalamu alaikum. Aminiya don Alah ku ba ni dama in yi kira ga manyan kasata Najeriya, da su dubi Allah su tuna nauyin da ke kansu. Daga Armaya’u Mai fetur da Gas, Tofa 08092100380.
Ga aminan Aminiya
Dobn Allah Editan Aminiya ka mika min sakon gaisuwa ga dimbin Aminan Aminiya, kuma masoyana. Duk ina yi muku fatan alkhairi. Daga Ummi T/Wada 07068743172.
Kukan yankin Daura
Aminiya ki isar da kukan mutanen yankin Daura da ke Jihar Katsina. Mu mutanen wannan yanki na Daura mun dade babu wutar lantarki, inda muka shafe kusan wata biyar ba labara. Amma ana samu a Katsina da Funtuwa. Ko mu an mance da mu. Daga Abubakar Salisu Maiaduwa 08126746353.
Addu’a ga kasa
Ya Allah Ka ba mu zaman lafiya a kasarmu Najeriya. Daga Aminu Jalo Sbn. 08138902520.