ManU ta dauki banja Milinkobic
Manchester United ta dauki mai tsaron gidan Serbia banja Milinkobic. Wannan shi ne dan wasan da kulob din ya saya a karon farko tun bayan korar Dabid Moyes a watan da ya gabata. Sai dai, Milinkobic, dan shekaru 17, zai kasance da FK bojbodina a kakar wasanni mai zuwa inda daga baya idan ya samu horo zai koma matakin manya.
Nemanja bidic da kuma Zoran Tosic su ne sauran ‘yan wasan Serbia da suka yi wa ManU wasa.
Barcelona ta yi sabon koci
Kulob din FC Barcelona da ke Sifen ya bayar da sanarwar yin sabon koci mai suna Luis Enrikue dan kimanin shekara 44 a ranar Litinin da ta gabata.
Wannan shi ne karo na uku da Koci Enrikue zai yi aiki a karkashin kulob din. Da farko ya taba yi wa kulob din kwallo a shekarar 1996 sannan a shekarar 2008 ne kuma ya zama koci mai kula da kananan yara a kulob din yayin da a halin yanzu kuma ya dawo a matsayin babban koci.
A yarjejeniyar da ya kulla Luis Enrikue ya sanya hannu ne a kwantaragin shekara uku. Enrikue ne kocin kulob din Celta bigo a kakar wasan da ta gabata inda ya taimakawa kulob din ya gama a matsayin na 9 daga jerin kungiyoyin da suka fafata a gasar rukunin La-Liga ta Sifen.
A karshen makon jiya ne tsohon kocin kulob din FC Barcelona Tata Gerardo Martino ya yi ban kwana da kulob din bayan ya kasa tabuka komai a kakar wasa ta bana inda kulob din ya gama kakar wasan bana ba tare da lashe wani kofi ba.
…Yayin da Luis ban Gaal kuma ya zama sabon kocin Manchester United
Luis ban Gaal ya amince ya zama sabon kocin kulob din Manchester United da ke Ingila da zarar an kammala gasar cin kofin duniya ta bana a Brazil.
Haka kuma kocin ya amince zai yi aiki da Ryan Giggs tsohon dan kwallo a kulob din a matsayin daya daga cikin mataimakansa.
Shi dai sabon kocin ya sanya hannu ne a kwantaragin shekara uku da za ta fara aiki da zarar an kammala gasar cin kofin duniya a bana.
ban Gaal ne zai jagoranci kasar Holand a gasar cin kofin duniya ta bana. Tun a ranar 21 ga Afrilun 2014 ne ya kulla yarjejeniya da kulob din na United amma kulob din bai sanarwa duniya ba sai a ranar Litinin din nan da ta wuce.
Tuni daya daga cikin ’yan kwallon United Rio Ferdinand ya nuna farin cikinsa a kan daukar ban Gaal a matsayin sabon koci kuma ya tabbatar kocin yana da kwarewar da zai taimaki kulob din wajen samun nasara a shekaru masu zuwa idan an ba shi hadin kai da goyon baya.
Gobe za a yi wasan karshe a tsakanin Madrid da Atletico
A gobe Asabar, idan Allah Ya kaimu, ne ake sa ran za a yi wasan karshe a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma ta Atletico Madrid dukkansu daga Sifen a gasar zakarun kulob-kulob na Turai watau UEFA Champions League.
Za a yi wasan ne a Lisbon da ke Fotugal. Wasan zai yi zafi ganin yadda dukkan kungiyoyin biyu suke hankoron lashe kofin.
Idan kulob din Real Madrid ya yi nasara, zai kasance ya lashe kofin sau 10 kenan yayin da kulob din Atletico Madrid kuma idan ya lashe zai kafa tarihi tun da bai taba lashe wa ba.
Idan za a tuna kulob din Atletico ne ya lashe gasar rukunin Sifen watau La-Liga a karshen makon jiya, don haka idan ya samu nasara a wannan karo zai hada manya kofuna biyu kenan a tsakanin mako daya.