✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A sha karatu lafiya Labarin Gizo-gizo da Kyankyanso da Fara

Barka da warhaka Manyan Gobe Ina fata Manyan Gobe na cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku guzurin labarin Gizo-gizo da Kyankyaso da…

Barka da warhaka Manyan Gobe

Ina fata Manyan Gobe na cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku guzurin labarin Gizo-gizo da Kyankyaso da kuma Fara. Ina fata za ku bi labarin bi-da-bi, sannan ku amsa tambayoyin da za su zo a karshen labarin.

A wani kauye mai yalwar bishiyoyi akwai wani uba da dansa da ke hira, yana ba dansa labarin gizo-gizo da kyankyaso da kuma fara, ya ce masa: “Gizo-gizo na da kafafu 8, kyankyaso kuma na da kafafu 6 da fuka-fukai 4, inda fara take da kafafu 6 da fuka-fukai 2, sai aka zuba wadannan kwari 18 a cikin keji ba tare da ka gani ba, amma jumullar kafafunsu 118, yawan fuka-fukansu kuma 40, don haka a yanzu ina so ka fada mini yawan gizo-gizo da kyankyaso da kuma farar da ke cikin kejin.”
dan nasa ya yi shiru, don haka ina so Manyan Gobe su turo mana da yawan gizo-gizo da kyankyaso da kuma farar da ke cikin kejin.