✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A sayo min Messi

A sayo min MessiWani mutum ne bakauye ya shiga cikin birni don ya ga yadda garin yake. Ya sauka a wajen mai shayi don ya…

A sayo min Messi
Wani mutum ne bakauye ya shiga cikin birni don ya ga yadda garin yake. Ya sauka a wajen mai shayi don ya karya sai ya tarar da matasa suna ta hira a kan wani dan kwallo amma shi bai fahimci abin da suke fadi ba. Suna ta cewa ya kamata a sayo musu Messi (dan kwallon Barcelona).  Bayan ya gama shan shayi ne a kan hanyarsa kuma sai ya kara jin wadansu matasa suna cewa ya kamata a sayo musu Messi. Nan ma abin ya ba shi mamaki. Ya sake zuwa waje na uku sai ya ji wadansu matasan su ma suna fadin a sayo musu Messi. Nan take ya koma gida inda ya kira dansa na fari ya ce ya kamata ya je kasuwa ya saro musu Messi, don da alama Messi zai yi tsada a kasuwa. Nan take dansa ya ce: “Ai Baba Messi dan kwallo ne, kuma ya iya kwallo shi ya sa ake cewa zai yi tsada a wajen sayarwa.”
Daga Ahmed Garba Mohammed, 08028797883

Ajiyar daji
Wani Bakatsine ne ya ci gasar MTN har Naira milliyan 10. Saboda kada mutane su san yana da wannan kudin, sai ya yanke shawarar kin ajiyewa a gida ko banki. Don haka sai ya tafi daji, ya samu gindin wata bishiya a cikin duhuwa, inda ba sosai mutane ke zuwa wajen ba, ya tona ya binne wannan kudin. Amma sai ya debi wani bangare na kudin  domin tafiya yawon shakatawa zuwa Indiya. Amma kafin ya bar wannan bishiya sai da ya samu waya, ya dauki hoton bishiyar nan don gudun mantuwa. Bayan ya je Indiya, ya sauka a wani otel tsawon sati daya. Rannan yana kwance a daki, sai ya dauko wayar nan, yana duba hoton bishiyar nan da ya binne kudinsa. Yana cikin dubawa, sai ya ga saman bishiyar nan ashe akwai wani mutum yana kallon duk abin nan da ya yi.
Daga Isah Ramin Hudu, Hadeja 08060353382

Kaza da akuya
Wata rana kaza da akuya sun fito yawo bakin titi, suna cikin tafiya sai wani mai mota ya taho da gudu ya fantsala musu ruwa. Sai kazar nan ta ce: “Mtss! Mutane haka suke tuki sai ka ce awakai.” Sai akuyar nan ta ce: Hhmm! Shi ya sa suke mutuwa kamar kaji.”
Daga Alhassan K. Idris Kafin Hausa, 08062936841