Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka CAF, ta zabi Casablanca, babban birnin Kasar Morocco, a matsayin inda za a yi wasan karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyyar Afirka ta CAF wanda zai gudana a ranar 17 ga watan Yulin 2021.
Kwamitin Zartaswa na Hukumar CAF ya cimma matsayar ce a karshen mako bayan taron da Shugaban Kwamitin Dokta Patrice Motsepe ya jagoranta ranar Asabar a Kigali, babban birnin Kasar Rwanda.
- An yi wa Ganduje rigakafin Coronavirus zagaye na biyu
- Biden ya yaba da yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Isra’ila da Falasdinawa
Za a fafata wasan ne a filin wasanni na Mohammed V Stadium, wanda ya kasance gida ga kungiyar Wydad da kuma Raja Casablanca.
Haka kuma, wasan karshe na gasar CAF ta kofin Confederations zai gudana ne ranar 10 ga watan Yulin bana a birnin Kwatano na Jamhuriyyar Benin kamar yadda mahukuntan suka zartar.
Hukumar ta kuma zabi Masar a matsayin kasar da za ta karbi bakuncin gasar cin kofin zakarun Afirka ajin mata da kungiyoyi takwas za su fafata cikinta, inda a nan gaba za a fayyace ranakun da wasannin gasar za su gudana a cikin wannan shekara.