✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A karshen watan Yuni za mu daina biyan tallafin man fetur —Ministar Kudi

An samu karin kashi 87 cikin 100 na hasashen abin da za ta samu a shekarar.

Gwamnatin Tarayya ta jaddada matsayarta cewa za ta dakatar da biyan kudin tallafin man fetur nan da karshen watan Yuni mai zuwa.

Ministar Kudi, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan yayin gabatar da tanadin kasafin kudi na 2023 ranar Laraba.

A cewar Ministar, gwamnati ta ware naira tiriliyan 3.36 ne kawai don biyan tallafin a wata shidan farko na sabuwar shekara.

Ministar ta ce matakin ya yi daidai da sanarwar da aka bayar tun a 2022 ta karin wa’adin cire tallafin zuwa wata 18.

Da take fayyace kunshin kasafin kudin, ministar ta ce kudin shigar da Najeriya ta samu zuwa Nuwamban 2022 sun kai naira tiriliyan 6.5, abin da ke nufin kasar ta samu karin kashi 87 cikin 100 na hasashen abin da za ta samu a shekarar.

Cikin kudaden da aka tara sun kunshi wanda Gwamnatin Tarayya ta tara na biliyan N586, Hukumar Kwastam ta karb naira biliyan 15, cibiyoyin karbar haraji masu zaman kansu sun tara tiriliyan 1.3, sai kuma sauran sashe-sashe da suka tara tiriliyan 3.7.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta APC za ta sauka daga mulki a karshen watan Mayu mai zuwa kuma dan takararta na Shugaban Kasa, Bola Tinubu, shi ma ya ce zai cire tallafin idan ya yi nasara a babban zaben 2023 “duk irin zanga-zangar da ’yan kasa za su yi.”

%d bloggers like this: