✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A hana Fulani tafiya da shanu zuwa Kudu – Ganduje

Gwamnatin Kano ta kaddamar da wani kwamiti wanda zai fito da tsarin yadda za a fara aiwatar da shirin samar da rugagen Fulani na zamani…

Gwamnatin Kano ta kaddamar da wani kwamiti wanda zai fito da tsarin yadda za a fara aiwatar da shirin samar da rugagen Fulani na zamani a jihar. Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya shaida wa BBC cewa shirin samar da ruga a Kano ba iya Fulanin da ke jihar ne kawai za su amfana ba, har da na sauran jihohin Najeriya.

Ya kuma ce shirin shi ne kawai zai kawo karshen rikici a tsakanin makiyaya da manoma.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce dole a sauya yadda ake gudanar da tsarin kiwo idan ana son magance  rikicin makiyaya da manoma. “Idan har ana son rigimar nan a daina ta dole a hana Fulani tafiya da shanu zuwa Kudu,” inji shi.

Ya kuma ce dole ne ya kasance a Arewa an yi wuraren kiwo ga duk wanda zai yi kiwon shanu.

Gwamnan ya ce shirin ruga a Kano ya kunshi samar wa Fulani hanyoyi na zamani ta hanyar ba ’ya’yansu ilimi da samar musu da asibiti da kuma banki na Musulunci da samar da kiwo na zamani dayadda shanu za su samu abinci domin samar da wadataccen nono.