✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A gidan mata

A gidan mata Wani Bafulatani ne ya je gidan mata, sai ya hadu da wani kawunsa. Sai ya ce wa kawun nasa: “Kawu ni ma…

A gidan mata

Wani Bafulatani ne ya je gidan mata, sai ya hadu da wani kawunsa. Sai ya ce wa kawun nasa: “Kawu ni ma na jo!” Kawun nasa ya ce masa: Me ka jo yi?” Sai ya amsa masa da cewa: “Na jo in yi jina!”
Daga Shitu Haris Zango Gwarzo, 07063482630

Addu’a a Makka

Wani Bafulatani ne ya je aikin Hajji, yana ta faman addu’a, sai ya ji wani Babarbare a kusa da shi yana cewa: “Ya Allah, duk abin da ka ba wa Bafulatanin nan, to ka ba ni biyunsa.” Sai nan da nan Bafulatanin nan ya ce: “Ya Allah, Ka manne mini ido daya.”
Daga Rayyan Jada

Direba da kwandasta

Wani kwandasta ne da direbansa suna cikin tafiya sai suka fara fada. Sai direban ya ce masa: “Kai jahili ne.” Shi kuma kwandastan ya ce: “karya kake.” Direban ya ce: “To idan kai ba jahili ba ne 2+2.” Sai kwandastan ya ce: “22.” Sai direban ya ce: “Wallahi gaya maka aka yi.”
Daga Umar S. Ahmad Fagge, 08036886870

Mahaukaci a kwana

Wani mahaukaci ne ya samu wata kwana da mutane suke shiga wurin fitsari ya tsaya, duk wanda ya rike sai duka. Rannan sai wani soja ya shiga, mahaukacin ya taso sai sojan ya shiga dukansa ba-ji-ba-gani. Da mahaukacin ya samu ya gudu sai ya tsaya gefen hanya, duk wanda ya zo shiga sai ya ce masa: “Ka yi hankali fa, akwai mahaukaci a kwana!”
Daga Ibrahim M. Tukur, 08097087341