✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A gaggauta yanke min hukuncin kisa —Abduljabbar

Kotun Musulunci ta kama fitaccen malamin nan, Abduljabbar Nasiru Kabara da laifin yin batanci ga Manzon Allah (SAW)

Fitaccen malamin nan, Abduljabbar Nasiru Kabara, ya nemi a gaggauta yanke masa hukunci bayan Kotun Musulunci ta kama shi da laifin yin batanci ga Manzon Allah (SAW).

A ranar Alhamis 15 ga watan Disamba 2022 Kotun Shari’ar Muslunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano ta tabbatar da laifin malamin, bayan wata 15 ana Shari’a a gabanta.

A yayin zaman kotun wadda Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ke jagoranta, Abduljabbar ya ce, “Ni ba na bukatar kai Ibrahim Sarki Yola ka yi min sassauci a wurin Allah kawai nake neman sassauci.

“Ina son a gaggauta zartar min da hukunci.

“Kuma ina amfani da wannan dama wajen ba masoyana hakuri kada su damu domin na san cewa zan yi mutuwa ta girma zan isa lahira a girmame.”