✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A gaggauta kammala masana’antar tiransfomar Najeriya —Buhari

Bayan kammalawa, kamfanin zai taimaka wajen bunkasa lantarki a Najeriya.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a hanzarta aikin kamfanin kera injinan tiransfoma a Najeriya don bunkasa wutar lantarki a kasar. 

Buhari ya ce so yake bayan kammalawa kamfanin ya rika samar da tiransfomomi da za su samu karbuwa a ko’ina a duniya.

“Buhari ya zaku kamfanin ya kammala don ganin irin cigaban da za a samu a fanin lantarki,” in ji Mataimakin Shugaban Cibiyar Bunkasa Harkokin Kimiyya (NASENI), Farfesa Mohammad Sani Haruna.

Ya kara da cewa bayan kammalawa kamfanin zai rika kera injinan tiransfoma masu karfin megawat tsakanin 6.5 zuwa 10 don cimma bukatun kasa.

Najeriya za ta yi aikin kafa kamfanin ne tare da hadin gwiwar kamfanin China Great Wall Industry Corporation (CGWIC) na kasar China.

Farfesa Muhammad ya bayyana cew annobar COVID-19 da ta addabi China ita ce ta haifar da jinkiri, in ba haka ba da aikin kafa kamfanin ya yi nisa.

“Sai mun fara kera wasu kayayyakin lantarki da kanmu ciki har da injinan tiransfoma kafin mu samu daidaito a fannin lantarki,” in ji shi.