Editan Aminiya ka ba ni dama in yi tsokaci kan dubarun tsaro 15 na Gwamna Shema na Jihar Katsina, indk ya yi bayani kan yadda za a shawo kan matsalar tsaro, musamman rikicin Boko Haram. Gwamnan ya bayyana wadannan dabarun tsaro ne a shafi na 50, a jaridar Ingilishi ta The Sun, a wata hira da aka yi da shi. A cewar Gwamna Shema, idan aka samar da wutar lantarki, aka hana shan miyagun kwayoyi da rashin aikin yi da laifufukan da ake aikatawa a tsakan kan iyakokin kasar, za a samu waraka daga tashe-tashen hankula, musamman Boko Haram.
Gwamna ya nuna takaicinsa kan yadda har yanzu ’yan matan Chibok ba su komo gida ba. Wannan na nuni da cewa Shema Shugaba ne na kwarai, musamman idan an yi la’akari da yadda ya damu da harkar tsaro.
Hakika wadannan dabarun tsaro 15 da yace sun jibanci inganta aikin gona da bai wa matasa horon sana’o’I, da gyara tarbiyya, don hana shan miyagun kwayoyi da aikata lafuka, ya zama dole a ce Mai girma Gwamna ya kara kaimi wajen aiwatar da su a Jihar Katsina da daukacin kananan hukumominta, ta yadda sauran jihohi za su koyi da mu. Daga Bilyaminu Sandamu Daura 08132511159
Ga Aminan Aminiya
Salam. Editan Aminiya ina maku fatan alherin da ke watan nan mai albarka. Allah Ya kara mana daukaka ya kuma kara mana zaman lafiya a kasarmu baki daya. Ina yi ma ’yan uwa da abokan Aminiya irin su Malam Lawal Shehu8 Daura da sauransu. Nagode. Daga Alhaji Yusuf Aliyu Maibara Jihar Katsina 08130457612.
Ga Edita da Aminan Aminiya
Edita ina mika gaisuwata a gareka da dimbin masoyan Aminiya. Allah Ya taimake mu amin. Daga Nafeesa dorayi Kanfako, Masalalcin Idi 08068073514.
Daular ISIL halartacciya ce
Rahoton jaridar Aminiya ta buga mai taken Malam Sunni sun ce Daular Isl haramtacciya ce,’ wannan ba daidai ba ne. Idan har jaridar Aminiya na son ta kubuta daga zargin da ake mata na cewa jarida ce da aka kafata kan akidar Shi’a, to ta hanzarta janye wannan rahoto. A maimakon haka, jaridar tana iya kawo rahoton Malaman Sunni da suke ganin Daular ISL ta halarta. Daga danlami Baban Tako 08030539506.
Murna a PDP
Salam Edita Juma’ar da za ta yi kyaut, tun daga Laraba ake ganeta. Ina taya dukkan ’yan PDP na Najeriya murnar lashe zaben Gwamna a Jihar Ekiti, saura na jihar Osun a watan gobe, da kuma gaba dayan Najeriya a 2015 insha Allah. Daga Isyaku Captain Kofa 08096209930/08114010050.
Ga Musulmin duniya
Assalamu alaikum. Edita, ina so ku jmika mini gaisuwa ga Musulmin duniya, maza da mata. Ubangiji Allah Ya karba mana ibadunmu, Ya kuma kankare mana zunubabbanmu. Daga Bilkisu Sani Adamu. 08033214285.
Sako ga mata
Salam. Edita ina so ka ban dama in mika sakona ga mata da mata me yasa in sallah ta zo ba su da kamun kai? Daga Angon Ummi Zariya 07063362550.
’Yan Arewa a yi zuciya
’Yan Arewa me yasa ba za mu yi zuciya ba, ku daina zuwa Kudu ana ci muku mutunci, bayan mu ma muna da abinci da za mu rika sayarwa a gida; ba sai kun tafi inda ba a sonku ba! Daga Fatima Sa’id Kano 07034445716.
Ga dan majalisa Galambi
Editan Aminiya ina fata za ka mika min godiyata ga Hon. Yusuf Galambi kan ayyukan taimakawa al’umma da yake kullum ba gajiyawa. Muna godiya Allah Ya daga likafa ta yi gaba. Amin. Daga Hussain Isa Basirka 08065880303.
Ga Zawiyyar Bunza
Ta’aziyyar Jama’ar Zawiyyar Bunza, kan rashin mahaifin Malam dansala. Da fatan Allah Ya jikanshi., Ya bai aMalam dansala hakuri da suarna jama’a. Allah Yasa mutuwa ta zasmo hutu. Daga Tela Bunza 07036107299.
Kira a Musulmi
Edita ina kira ga Musulmi da su yi amfani da kwanakin wannan watan don yin addu’a t amusamman ta neman zaman lafiya a Najeriya. Daga H. S. KArkarna 08034543843.
Ga Shekarau
Ina taya Maigirma Sardaunan Kano, Malam Ibrahim Shekarau murna, bisa samun ministan ilimi day a yi. Allah Ya taya shi. Amin Daga Abubakar Umar Kofa 08065746051.
Ga Aminan Aminiya
Fatan laheri ga daukacin masoyabn Aminiya. Allah Ya taimakekmu daga Nafeesa Abubakar Bichi 08068073514.
Ga ’yan majalisar Adamawa
Assalamu alaikum. Edita, tsige Gwamnan Adamawa da ’yan majalisa suka yi babu mamaki. To su da wanda ya sanya su, in Allah Ya yarda za su bar mulki. Kowa ya yi da kyau kansa. Domin za ku gane kurenku, tunda Allah Yana bayan mai gaskiya. Daga Maimagani U/Zagi, Mashi, Jihar Katsina 07052553976.
Ga ’yan mjalisar tarayya
Tsige Gwamnan Adamawa, Murtala Nyako kiyayyace karara, don haka kuma ‘’yan majalisar tarayya ku tsige mana Jonathan, tunda ya aikata ayyuka da suka saba wa doka, ga kabilanci da raba kan al’umma. kalubalenku. Daga Ibrahim Custom, Mai APC, Sabon garin Zariya.
Adu’ar Ramadana
Ina mika godiyata ga Allah (SWT) da ya nuna mana wannan wata mai albarka. Aminiya ina yi muku adu’a ku da ma’aikatanku. Allah Ya ba mu albarkacin watan Ramadana. Daga Bello Adamu Bajoga 08028787485.
Tsige Nyako kalubale ne
A gaskiya tsige Murtala Nyako daga gwamna kalubale ne ga siyasar Najeriya. Daga Nasiru Bello Gusau 07068223562.
Ta’aziyya ga Sarkin Hadeja
Aminiya ina yi Maimartaba Sarkibn Hadeja ta’aziyyar Shamakinsa. Allah Ya jikansa. Daga Bin Usman Gumel 07034852558.
Sudan ishara ce
Salam Edita yaya azumi. Ga sakona ga ’yan kasata, cewa mu zauna lafiya, mu hada kai. Kai Sudan ta ishemu ishara. Daga Ali Garba Harbo 08056444726.
Ga Sheikh dahiru Bauchi
Edita ka mika min gaisuwata ga Sheikh dahiru Usman Bauchi. Allah Ya kara masa lafiya. Daga ‘Yan Kafachan 09094280064.
Jinjina ga Kwankwaso
Allah Ya kawo mana kai a Shugaban kasar Najeriya. Amin. Daga Alhaji Rayyanu Papa, sarkin Yakin Kwankwaso insha Allahu. 08052936945.
Addu’ar talakawan APC
Mu talakawan jam’iyyar APC, Alhamdulillahi, Allah Ya karbi addu’armu, Ya cire mana munafukai. Bafarawa da Shekarau da Sharriff duk sun fice. Daga Ahmad Rufa’i Kalli Maiduguri 08025580232.