✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘A dokar Najeriya, laifi ne rama marin dan sanda’

'Ko da ya mare ka, bai kamata ka rama ba'

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya CSP Olumuyiwa Adejobi, ya ce babu dokar da ta ba wani damar rama marin da dan Sanda ya yi masa.

Kakakin ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter, inda ya ce duk wanda yake ganin dan sanda ya yi masa laifi, to ya shigar da kara ga hukuma, ba wai ya dauki doka a hannunsa ba.

Kakain dai na wannan  bayanin ne kan wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, na wani mutum da ke ja-in-ja da wani dan sanda da ke kokarin kwace masa waya.

Adejobi ya ce duk wanda ya mari dan sanda, ba rundunar kawai ya yi wa rashin da’a ba, har da kasarsa.

“Ko da dan sanda ya ci zarafinka. musamman idan da kayan aiki a jikinsa, to rashin girmama kasa ne ka yi masa duka.

“Hakan babban laifi ne a dokar Najeriya.

“Saboda haka yanzu ba batun cin zarfin da dan sandan ya yi ake yi ba, na rashin ladabin da ya nuna masa ne da ya rama.

“Balle ma kokarin kwace wayar ba wani abu ne mai wuyar kai rahoton ba, ko daukar mataki.

“Yanzu muna tsare da wadanda suka aikata laifin a wani otal, kuma ranar Litinin za mu gabatar da su a gaban kotu.