✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A daina sakin ’ya’ya kamar dabbobi – Kwamishinan ’yan sanda

Kwamishinan ’yan sadan Jihar Kuros Riba Hafiz Muhammad Inuwa ya gargadi iyayen yara da su  rika sa ido, tare da  jan kunnen ’ya’yansu domin kada…

Kwamishinan ’yan sadan Jihar Kuros Riba Hafiz Muhammad Inuwa ya gargadi iyayen yara da su  rika sa ido, tare da  jan kunnen ’ya’yansu domin kada su rikide su zama batagari, musamman yadda ake yawan samun gurbacewar tarbiya da ake zargin matasa. Hafiz ya yi wannan gargadi ne a ganawar da ya yi da manema labarai, lokacin da ya  gabatar musu da rikakkun ’yan fashi da makami da aka kama aka kai su    ofishinsa. 

A cewarsa: “Gargadin da zan yi wa iyayen yara a jihar nan da su rika kula da takun ’ya’yansu, su san abokansu da kuma irin abubuwan da suke shigo musu  gida da su, wadanda ba iyayen suka ba su ba, sai su rika tambayar su. Har wayau su daina barin ’ya’ya sakaka kamar dabbobi.”

“Rundunata ba za ta bari duk wani batagari ko dan ta’adda ya ci Karen sa babu babbaka a Jihar Kuros Riba, “ inji shi.

A kalla mutum 17 aka nuna wa ’yan jarida da aka kama ake zarginsu da aikata miyagun laifuka daban-daban da suka hada da kama mutane ana garkuwa da su da kuma fashi da makami a wurare daban-daban ciki da wajen birnin Kalaba.

An kama wasunsu da kananan bindigogi da kayan tsubbu  da kanana bindigogi kirar gida da harsasai, don haka ya ce kotu za a mika su da zarar an gama bincike.

Iyamba Iyamba wani daga cikin wadanda ake zargi da fashi da makami ya shaida wa Aminiya cewa: “Ni ba fashi na yi ba, daga na tona wa wani jami’in tsaro asiri ne yana fataucin kwayoyi, ya ce sai na ga abin da zai yi mini, shi ya sa aka kawo ni nan aka hada da ’yan fashi.”

Cikin kayan da barayin ake zargi sun sato sun hada da manyan akwatunan talbijin da wayoyin hannu.