✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A alkinta karatun Sheikh Isa Waziri

Editan Aminiya, ka ba ni dama in yi ta’aziyyar Sheikh Isa Waziri, Wazirin Kano. Allah Ya gafarta masa, Ya kuma kyauta karshenmu. Amin. Sannan ina…

Editan Aminiya, ka ba ni dama in yi ta’aziyyar Sheikh Isa Waziri, Wazirin Kano. Allah Ya gafarta masa, Ya kuma kyauta karshenmu. Amin. Sannan ina bayar da shawara ga SKY da Alhaji Salisu Sambajo da sauran masu kudi da ke daukar nauyin karatunsa a gidajen rediyo, da su taimaki al’umma wajen alkinta karatun wannan shehin malamin a faya-fayen CD da DbD da memory cards, ta yadda za a ci gaba da amfana da tafsirinsa. Irin wannan aiki ba sabon al’amari ba ne, domin an yi wa karatu da wa’azin Marigayi Malam Jaafar Mahmud Adam da Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi. Allah Ya ba da ikon yin wannan gagarumin aiki, don amfani al’ummar Musulmi. Daga Sanin Bola (Joe) Fagge Kano. 08168555872.

Sakonnin waya

Barka da Sallah
Assalamu alaikum Edita ina yi wa al’ummar Musulim duniya barka da salla, musamman masoyan janar Buhari, Shugaban kasar Gobe in Allah Ya yarda. Daga Ruky Bala Fagge 08101244290.

Ga mawaki Ibrahim A. Jiwa
Salam Aminiya, don son Annabi ku isar mini da sakona ga mawaki Ibrahim A. Jiwa, ko ya daina waka ne. Daga Khadija Kaduna Tudun Wada. 08099484499.

Ga Sule Lamido
Aminiya ina so ku mika kukana ga Gwamnan Jigawa don ya biya mu hakkin mu, ya tuna fa wata rana sai wasu. Nagode. Daga Hon. Saminu Sule Madu. 07030122539.

Ga sabon Shugaban Mali Keita
Ina tanya sabon shugaban kasar Mali Ibrahim Bubakar Kaita Murnar lashe Zabe.Allah ya bashi ikon yin adalci a wajen jagorantar ‘yan kasar.Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi tashar bagu Gusau

Tunatarwa
Sallama. Aminiya mai farin jini da fatan an yi sallah lafiya, tunatarwa ga Musulmi, mu rike ibada da son juna da kishin Arewa. Allah ka ba mu zaman lafiya. Daga Malam Kabiru Hamdala Gusau. 08066272283.

Ina ’yan uwan Ariel Castro?
Editan Aminiya da fatan za ka binciko yaya aka yi da ’yan uwan Castro biyu da aka kama su tare da laifin boye ’yan mata uku a wani gida, har shekara 10. Ko su ba a same su da laifin komai ba? Ku ne kuka buga wannan labari a can baya, har da hotunansu, su uku da ’yan matan uku. Daga Zauro Abdullahi Sakkwato 08069077363.

Martanin durkushewar Arewa
Naji dadin rubutun Bello Linguist Sokoto Cinema, na ranar 09-08-013, a kan durkushewar Arewa. Ya fadi gaskiya, amma ai matsalar na gun manyan Arewa. Mutumin Arewa zai fito takarar Shugaban karamar Hukuma ko dan majalisa, idan ya ci zabe hatta mutanen garinsu, ya manta da su. Daga AbdulMalik Kabir Ghude. 08056717265.

Ga Matawallen Kazaure
Sako ga dan Majalisar Jihar Jigawa, kuma Matawallen Kazaure, Alhaji Bashir Adamu. kungiyar masu kishin kasa ta Kazaure na mika gaisuwar sallah ga Matawallen Kazaure da fatan ka yi sallah lafiya. Muna yi maka fatan alheri, musamman ganin irin ayyukan raya kasa da ka aiwatar a masarautar Kazaure da tallafa wa jama’a maza da mata. kungiya na addu’ar Allah Ya sa ka zama Gwamna Jihar Jigawa a shekarar 2015 mai zuwa. Amin. Muna mika fatan alheri ga Alhaji Mabo Shugaban PDP na karamar Hukumar Kazaure. Allah Ya tabbatar da nufinmu.
Daga Malam Malam Sani Mai Rediyo, Kazaure. 08067340868.

Ga Iyar Zamfara
Salam don Allah Edita, ina son ka ba ni fili domin in yi jinjina ga matar gwamnanmu n Zamfara, wato Hajiya Khadija Abdul’Aziz Yari Abubakar, Iyar Zamfara, Iyar Shinkafi, kilishin Garewan Tsafe, kuma Gimbiyar Maradun, bisa ga taimakon da take yi wa al’ummar Jihar, musamman ga mata, ya zama dole a yaba mata, kan kokarinta a watan Ramadana. Daga Muhammad Hassan. Danbaza , Zamfara, Radio Gusau.

Ta’aziyyar mutanen Barno
Kisan da aka yi a masallacin Barno abin kunya ne ga Najeriya. Al’ummar Barno ina mika ta’aziyyata gareku. Allah Ya jikan wadanda suka mutu. Amin. Daga Auwalu Musa Ibrahim Warure (Auwalun Madrid). 08066885356.

Ga Malaman Jami’a
Salam. Ya kamata Malaman Jami’a su koma bakin aikinsu. Daga 07034754993.

Jan hankalin direbobi
A miniya don Allah ku aika sakona zuwa ga direbobin mota das u dubi girman Allah su rika tsayawa, suna gabatar da sallah a lokacin da suka dauko fasinjoji. Domin babu uzuri garesu. Daga Abu Ja’afar Usman Ibrahim Nadabo kankara. 07068353836.

Gwaggwabar lada
Annabi (SAW) ya ce duk wanda ya azumci watan Ramadan, sa’annan ya biye  da azumin shida cikin Shawwal kamar ya azumci shekarar ne gaba daya. Ya dan uwa kada a barka a baya, ga gaggauta ka kwashi garabasar Ubangiji da gwagwabar lada. Daga Auwalu Yayan Fati 08120646429.

Dole mu bar PDP
Shin Gwamna Lamido ina ka dosa ne, kai da kanenka Gwamna Kwankwaso? Domin PDP ba ta da niyar yi mana adalci, ya zama dole mu barta, tunda shegiyar uwa ce. Daga Ahmed Fada 07065550587.

A bai wa Buhari takara
Aminiya ’yar mana, ki gaya wa uwar jam’iyyar APC ta kasa, amtukar suna son goyon bayan talakawan Najeriya, to su bai wa Janar Muhammadu Buhari takara a shekarar 2015, domin kawar da halin kunci da jam’iyyar PDP ta jefa ’yan Najeriya. Daga Musa U/Mai Yasin danja, Jihar Katsina 08155648155.

Dubi kisan gilla a Najeriya
Allah Sarki dubi yadda ake kisan bayin Allah a kasata Najeriya, babu gaira, babu dalili, kamar ba za a je kiyama ba. Daga Isah Kwafsi Asarara Shagari Sakkwato.  07033427207.

Bafarawa da Buhari na APC
Sakkwatawa kuna tare da adilai a jam’iyyar APC, irin su Bafarawa da Buhari da farfesa Maishanu YAbo. Allah Ya taimake su amin. Daga Musty Sok. 08034068363.