Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce jihar Jigawa ce ke kan gaba a jihohin da ke fama da talauci a Najeriya inda kaso 73.9 na yaran jihar ke rayuwa cikin kangin fatara.
Bayanin hakan na kushe ne a cikin wani rahoto na sakamakon bincike mai lakabin MICS 6 da asusun ya gudanar a Kananan Hukumumomin jihar 27 a shekarar 2021.
- Kamfanin jiragen sama ya fara zirga-zirga daga Abuja zuwa Jigawa
- Najeriya ta fi kowace kasa yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya – UNICEF
A jawabinsa yayin taron gabatar da rahoton, mai kula da ofishin shiyya na asusun a Kano, Rahama Mohammed Farrah ya ce, rahoton sakamakon binciken na da matukar tayar da hankali.
Ya ce rahoton ya nuna karara irin mummunan halin rayuwar yara a jihar ke ciki, da kuma yadda za su kasance nan gaba.
“Yawancin yara a jihar an hana su hakkin da su ke da shi na rayuwa mai kyau da kariya da kuma ci gaba mai amfani,” inji Rahama
Rahoton ya kuma nuna cewa kaso 65 na yara a jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya na cikin kangin fatara idan aka kwatantasu da sauran yaran da ke sauran sassan kasar.
Sai dai rahoton ya yaba wa jihar bisa nasarar da ta samu na riga-kafin yara a inda mace-macen da ake samu a cikinta ya ragu da kaso 37 a tsakanin yara ‘yan kasa da shekara biyar.