Kwararan majiyoyi sun tabbatar wa Aminiya cewa dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, na kokarin daukar tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a zaben 2023.
A bangare guda kuma, babban abokin karawar Tinubu, Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, na shirin daukar Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta a matsayin mataimaki.
- Jiga-jigan tsohuwar jami’yyar CPC na son Malami ya zama abokin takarar Tinubu
- Boko Haram ta yi garkuwa da mata 2 a Konduga —‘Yan sanda
Majiyoyinmu sun tabbatar da cewa idan har al’amura ba su sauya ba, Atiku zai sanar da daukar Ifeanyi Okowa, shi kuma Tinubu zai dauki Kashim Shettima a matsayin dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa.
Zuwa yanzu dai kwana uku kacal suka rage kafin cikar wa’adin da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ba su na mika mata sunayen abokan takararsu.
Tun bayan kammala zaben ’yan takarar shugaban kasa na manyan jam’iyyun biyu, hankula suka koma kan ganin wadanda za su zama abokan takarar Atiku da Tinubu.
Masu sharhi sun bayyana cewa zabin abokan takarar zai taka muhimmiyar rawa wajen yin alkalanci tsakanin manyan ’yan siyasar biyu a zaben 2023.
Zabin Shettima
Majiyoyinmu masu tushe daga cikin makusantan Tinubu sun ce ya riga yanke shawarar zabar Sanata Kashim Shettima, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen tallata aniyarsa ta zama dan takaar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, a matsayin abokin takararsa.
“Asiwaju ya natsu da Sanata Shettima, saboda rawar da ya taka wajen ganin Tinubu ya zama dan takara.
“Sannan Shettima mutum ne da ke da karbuwa a sassan Najeriya, saboda yadda ya kulla alaka tsakanin sassan Najeriya a lokacin da yake Gwamnan Jihar Borno da kuma a Majalisar Dokoki ta Kasa a matsayin Sanata.”
Wata majiya a Fadar Shugaban Kasa ta ce duk gwamnoni uku da APC ke da su a yankin Arewa maso Gabas na goyon bayan Shettima.
“Buhari ba ya adawa da zabin Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu,” inji majiyar ta Fadar Shugaban Kasa,” inji shi.
Ta ce, “Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Shettima babban mai goyon bayan Shugaba Buhari ne.”
Ta bayyana cewa hatta ayyuka da nasarorin da Shettima ya samu yakan danganta su da goyon bayan da ya samu daga Shugaba Buhari.
“A zabukan 2015 da 2015 ya kawo wa Buhari tulin kuri’u daga Jihar Borno da sauran jihohin yankin Arewa maso Gabas.
“Sannan yana da cikakken goyon bayan gwamnonin APC uku da yankin ke da su; Babagana Zulum na Jihar Borno, Mai Mala Buni na Jihar Yobe da kuma Inuwa Yahaya na Jihar Gombe.
“Lokacin da Tinubu ya ziyarci Jihar Borno, Zulum ya shaida mishi cewa ba ya sha’awar zama mataimakin shugaban kasa, ya kuma bukace shi da ya dauki Sanata Shettima a matsayin abokin takara,” inji majiyar.
Ta ce idan har Tinubu ya zabi tsohon Gwamnan Jihar Bornon, to lissafin siyasar ya yi daidai domin, “Zai zama takara ce da ke damawa da kowane bangaren Najeriya ta fuskar siyasa da addini da shekaru da bangare da sauransu.
“Shettima ya bayar da muhimmanci ga samuwar zaman lafiya da rungumar juna lokacin da yake Gwamnan Jihar Borno, inda ya kashe sama da Naira biliyan daya wajen gyaran coci-coci da Boko Haram ta lalata.
“Sannan, yawan Kiristocin da ya dauki nauyinsu shi kadai zuwa Ibadar ziyara zuwa Birnin Kudus ya fi yawan wadanda jihohin da Kiristoci suke mulki a Arewa irin su Binuwai da Filato da Taraba suke daukar nauyinsu.”
Sai dai kuma Aminiya ta gano cewa akwai gwamnoni uku masu ci a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya da kowannensu ke son zama abokin takarar Tinubu.
Gwamnonin su ne Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, Muhammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa da kuma Sanata Abubakar Atiku Bagudu na Jihar Kebbi.
“Amma APC ta fi so ta fitar da mataimakin shugaban kasa daga yankin Arewa maso Gabas domin ta raba kuri’un da Atiku zai samu a yankinsa.”
Bangaren CPC
Sai dai kuma bangaren tsohuwar Jam’iyyar CPC da suka hade aka kafa jam’iyyar APC na shirin gabatar da Ministan Shari’a, Abubakar Malami a matsayin wanda za a dauka ya yi wa Tinubu mataimkai.
“Bangaren CPC na neman Buhari ya sanya baki ta hanyar nuna goyon bayansa ga Abubakar Malami ko Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika a matsayin abokin takarar Tinubu,” a cewar majiyar.
Sai dai ta ce, “Bisa dukkan alamu shugaban kasa na so ya maimaita irin abin da ya yi a lokacin babban taron APC; zai saurari kowane bangare amma zai iya barin dan takarar ya zabi wanda yake so ya zaba…
“Za su yi aiki tare wajen fito da dan takarar da zai kawo musu yawan kuri’u domin cin zabe, wanda shi ne babban burin APC,” inji majiyar.
Wata majiya ta ce Tinubu zai yi wata ganawa da Shugaba Buhari a ranar Talata, inda ake sa ran zai tattauna batun abokin takararsa.
Daga Sagir Kano Saleh da Ismail Mudashir da Baba Martins